https://maannews.acnoo.com/public/uploads/images/ads/adds.jpg

KANSILOLIN KARAMAR HUKUMAR BATSARI SUN TUMBUKE SHUGABAN SU...

top-news

Daga: Abdulkadir Nafiu 

A yau Juma'a 13/10/2023 kansilolin karamar hukumar Batsari sun tumbuke shugaban kansilolin karamar hukumar Sanusi Sale daga matsayin sa na shugabansu....

Tumbukewar ta biyo bayan kwararan hujjojin da kansilolin suka bayyana matsayin dogaron su ga yanke wannan hukuncin....

Na daga cikin hujjojin sun hada da,maida kansilolin karamar hukumar wata saniyar ware,duk wasu ayyuka da doka tabasu damar aiwatarwa matsayin su na kansiloli shugaban karamar hukumar baya basu dama,na daga cikin ayyukan sun hada da,Kasafin kudi da tsare-tsare na karamar hukumar, aiwatar da wasu ayyuka a fadin karamar hukumar da gwamnatin jiha take bayarwa,zargin karkatar da kudin shiga,wato(Revenue) na karamar hukumar ba tareda sanin inda kudin suke zurarewa ba....

Wani dalilin ma shine,babu Kansila guda da yake da mazauni a sakatariyar karamar hukumar, sa'annan kimanin kansiloli goma(10) a cikin Sha daya(11) sunkoka ga yadda shugaban karamar hukumar keyin watsin Allah-tsine da koken su wanda suke karbowa daga bakunan talakawan su na Kauye da ya shafi ilimi,lafiya da sauransu....

Wakillan mu da suka halarci taron tsigewar a yau da ya guda na a sakatariyar karamar hukumar ta Batsari,wakillan namu,sun shaida yadda Clark na karamar hukumar ya bayyana cewa su kansu basajin dadin zagayewar da ake masu wajen ayyuka da tsare tsare a gwamnatin karamar hukumar....

Sai dai anjiyo cewa shi kansa tsohon shugaban kansiloli na karamar hukumar Hon Sanusi Sale, ya bayyana cewa ashirye yake ya ajiye mukamin nasa,saboda shi kansa shugaban karamar hukumar baya jin shawarar sa,kuma uban gidansa ne ba zai iya takura shi ba kan wasu abubuwan inji Sanusi Sale....

Bayan tumbuke tsohon shugaban kansilolin Sanusi Sale,duk a yau din dai, kansilolin sunkuma zabi Hon Sanusi Sani na gundumar Darini/Magaji Abu matsayin sabon shugaban kansilolin karamar hukumar ta Batsari da zai maye gurbin Hon Sanusi Sale ga shugabancin kansilolin karamar hukumar....

Wannan dai shine lamari mafi muni da gwamnatin karamar hukumar Batsari ta fuskanta tun bayan zaben kananan hukumomi a shekarar 2022.
Katsina Online 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *