Sashen ofishin mai baiwa Gwamna shawara akan samar da ayyukan yi da inganta su na Jihar Katsina na sanar da duk 'yan asalin Jihar Katsina.
- Katsina City News
- 09 Oct, 2023
- 875
Masu sha'awar shiga aikin sojan Najeriya maza da mata masu Sana'a da wadanda basu sana'a an fara cike fom din neman aikin ta yanar gizo daga ranar 25/9/ 2023, zuwa 20/10/2023, ta sashen hanyar daukar ma'aikatan soja kamar haka, https://recruitment.army.mil.ng.
2- Duk mai neman aikin dole ne ya mallaki akalla passes guda 4 mafi karanci daga cikin Jarabawar karshe ta gama sakandire WASCE, GCE, NABTEB da NECO.
3- Masu nema dole ne su kasance su na da takardar shaidar zama yan asalin jihar Katsina.
4- Sashen kuma yana son a sanar da duk masu neman cewa dole ne su kasance masu lafiyar jiki, da hankali lafiyayye, kuma ba su da wani laifi da dokar kotu ta yanke masu hukunci.
5-Ma'aikatan jinya da ungozoma wadanda basu wuce shekaru 30 ba suma suna iya nema.
6- Masu nema dole ne su mallaki takardar shedar ta asali.
7- Za a gudanar da tantance wadanda za a dauka da su ka fito daga Jihar Katsina daga ranar 6 zuwa 19 ga Nuwamba 2023, a barikin sojoji dake Natsinta, bisa hanyar zuwa Jibia Katsina, Jihar Katsina Najeriya.
8- Don ƙarin neman bayani game da cikakkun bayanan daukar ma'aikatan sojan ana shawar tar masu nema su duba sashen yanar gizo na daukar ma'aikatan soji.
Watau https://recruitment.army.mil.ng. a hankali ko kuma a kira wadannan lambobin idan kuna da wani shakku 07081271986 da 07041467033.
Sannan kuma za ku iya tuntubar hedkwatar sashen hukumar samar ayyukan yi da ke bayan gidan Labo Tarka GRA katsina. Ko kuma a kira daraktan kula da samar ayyukan yi ta wannan lamba 08035873222 ko kuma a kira daraktan yada labarai na hukumar akan 0703503335.