BAYAN HUKUMCIN KOTU: An sanya Dokar Taɓaci awa 24 a Kano

top-news

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 24, bayan yanke hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ɗauke da sa hannun kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ta ce dokar ta fara aiki ne daga ƙarfe shida na yammacin ranar Laraba zuwa shida na maraice ranar Alhamis.

'Yan sanda sun ce an sanar da gwamnatin jihar game da wannan mataki a cikin wata wasiƙa da aka aika mata.

CP Mohammed Usaini Gumel, ya ce jami'ansa da haɗin gwiwar sauran jam'ian tsaro, za su yi sintiri a lungu da saƙo na Kano, domin tabbatar da bin doka da oda.

Sanarwar ‘yan sandan ta yi kira ga al’ummar Kano su bai wa wannan mataki hadin kai.

Haka kuma rundunar ta gargaɗi mutane game da karya dokar, tana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci

NNPC Advert