An kammala gina aikin hanyar data tashi daga Masallacin Juma’a na GRA gidan dawa tabi ta makabarta zuwa titin ring road.
- Katsina City News
- 29 Nov, 2024
- 1399
Aikin na daga cikin ayyuka ukku na tituna da Dan Majalisar tarayya Hon Sani Aliyu Dan Lami yake gudanarwa a halin yanzu a karamar hukumar Katsina.
Sauran ayyukan hanyar sun hada da wadda tabi ta bayan gidan gwamnati a modoji sai wadda tabi ta bayan Customs base a cikin GRA da kuma Layout akan titin Dr Garba Shehu Matazu.
Ayyukan na daga cikin kokarin da Sani Aliyu Dan Lami yakeyi na inganta rayuwar al'ummar karamar hukumar katsina.