Daga Ɗanjuma Katsina
Mutane kashi-kashi na faɗin ra’ayinsu kan sulhu ko zaman sasanci da ’yan bindiga, miyagun mutane masu ɗauke da makamai, masu aikata mummunan aiki wanda ko dabbobi ba sa yi.
Akwai masu ra’ayin a ci gaba da yaƙi da su har sai an ga bayansu, kar a saurare su, su ji wuta kawai. Duk wata matsaya ba wannan ba, to ba su tare da ita.
Irin wannan zafin ra’ayi shi ne matsayar Gwamnan Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa kafin ya ci zaɓe da kuma bayan hawansa; za ka ga idan yana magana jikinsa na rawa, bakinsa na kumfa.
Masu wannan ra’ayi, tsakaninsu da Allah suke, kuma iyakar gaskiyarsu suke faɗa.
MATSALAR WANNAN MATSAYA
Jami’an tsaronmu suna da kishin yaƙi da waɗannan miyagun mutane, amma suna ƙarƙashin dokoki da ƙa’idojin yaƙi. Suna bin umurni ne, sai an ce musu, kuma jami’an tsaron ƙasa masu kayan aiki na zamani da kariyar doka suna ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya ne. Suna da ƙarancin yawan ma’aikata, suna kuma da raunin kula da lafiyar iyali ko lafiya idan wani abu ya same su a wajen aikinsu. Don haka suna cikin tarnaƙi.
Malam Dikko Raɗɗa ya riƙa kalamai kan tsaro, amma bayan ya hau, wasu lamurra suka bayyana masa, ya gani ƙuru-ƙuru cewa Gwamnatin Jiha ita kaɗai ba za ta iya maganin matsalar ’yan ta’adda kashi 60 cikin 100 ba.
Ya fahimci cewa hatta ɗan sandan da ke tsayawa bayansa yana yi ne bisa umurni. Duk ranar da aka ba shi akasin umarni, to zai canza. Babu wani Gwamna, ko da shi wane ne, da ke da iko da ɗan sanda ɗaya ko DSS ko soja, sai dai dokar da ta ba su aiki, ko kuma ya nemi alfarma.
Wannan ta sa ya kafa jami’an tsaron al’umma, su ma bisa dokar da ƙasa ta ce a kafa su. Sai kuma taimakon jami’an tsaron Tarayya don su yi aikinsu, ta hanyar taimaka musu da abin da suke buƙata na kayan aiki. Amma bai iya ba su umurni ba, sai dai neman alfarma, sai kuma wasu hanyoyin ƙarfafa al’ummar da abin ya shafa.
Masu ra’ayin a yaƙi ’yan ta’adda har a ga ƙarshensu suna yin haka ne cikin kishi da takaici, amma ba su san wasu tarnaƙin da ke tattare da hakan ba.
’Yan ta’addar nan miyagu matsorata ne, suna cikin daji a warwatse. Waɗanda suka addabi ƙauyukan da ke cikin daji ne, inda ba motocin yaƙi ke isa wajensu cikin sauƙi ba. Jirgin sama kuma sai an cika takardu, umurni ya zo.
Wannan ya sa ƙauyukan da ke kusa da su ba su da wani zaɓi sai dai su yi sasanci da su.
Wata matsala kuma ita ce, miyagun nan suna da muggan makamai tare da su. Suna shan ƙwayoyi, duk wata ƙwaya ko hoda da ka sani ana kai musu ita a daji suna sha. Idan suka sha, sai hankali ya fita, su zama kamar dabbobi, sun ma fi dabbobi rashin hankali, yayin da mutanen da ake kai wa hari ba su da waɗannan makamai, ba su kuma shan ƙwaya.
Ƙarin tarnaƙi shi ne, ɓarayin nan na daji tantiran jahilai ne, na gani a ba da labari.
Waɗannan na daga cikin dalilan da ke sanya ƙauyukan da ke kusa da dazuzzukan da ɓarayin suke yin sasanci da su.
Wasu har su zama masu kai musu labari.
MAFITA GA ƘAUYUKA
Idan da za a ce duk lokacin da mutane suka nemi ɗauki za su iya samu cikin gaggawa, da ana kai faɗa har tsakiyar daji a yaƙi ɓarayin dajin inda suke a hana su sakat.
Da ana ɗaukar matakin duk harin da ɓarayin daji suka kai, a rama musu da martani mai zafi da ba za su sake tunanin kai hari ba. Da mutanen ƙauyuka da garuruwa za su samu ƙarfin gwiwar tunkarar duk wani hari da aka kai musu.
Ko a wannan ma sai idan an samu tallafin jami’an tsaro, domin muna da misalin garuruwa kamar biyu da suka dage suna kare garinsu, amma ɓarayin suka yi musu gangami suka yi musu mummunar ta’addanci: a Batsari da kuma Mantau a Malumfashi.
KO ANA SULHU DA ƊAN TA’ADDA?
Wannan tsari ne na tsaron duniya da gari kan gari. Ana amfani da tubabbun ’yan ta’adda a yaƙi waɗanda ba su tuba ba.
Ana amfani da tsofaffin masu safarar miyagun ƙwayoyi a yi yaƙi da waɗanda suke cikin safarar.
Ana amfani da waɗanda suka amince da tsarin sulhu su kare inda ake buƙatar zaman lafiya.
Duk wannan ana yin sa ne cikin tsari da ƙa’ida.
Amurka ta yi yarjejeniya da ’yan Taliban ta miƙa musu mulkin Afghanistan, ita kuma ta bar ƙasar.
Bayan shekaru 20 tana yaƙi da Taliban, ta gane cewa su ne kaɗai za su iya zaunar da ƙasar lafiya, dole ta zauna da su ta bar musu ƙasar.
Shugaban ƙasar Siriya na yanzu shi ne ɗaya daga cikin shugabannin ’yan tawaye masu tsattsauran ra’ayin addini. Duniya ta shirya da shi yanzu, shi aka bar wa ƙasar.
Ƙasar Saudiyya ta sha amfani da mutanen Yemen da ke ƙasarta wajen yaƙar masu neman ganin bayan sarautar ƙasar.
Misalai suna da yawa a duniya, da kuma yaƙe-yaƙe a wurare daban-daban.
Don haka sulhu da ɗan ta’adda bisa tsari, sharaɗi da ƙa’ida ba laifi ba ne a siyasar duniya da kuma tsarin tsaro na duniya.
SULHUN AL’UMMAR KATSINA
An fara shi a ƙaramar hukumar Jibiya, kuma sai da ya yi shekara cif ba matsala. Daga nan ya watsu zuwa wasu ƙananan hukumomi.
Bayan yin shi, an samu ragi sosai na korar gari a kai mutane daji, ko tare hanya a kwashi mutane daga mota zuwa daji, ko kai hari don kisa.
Amma ɓarayin dajin sun ci gaba da fashi, kwace shanu, da cin ƙarfi a ƙauyukan da ke kusa da su. Za su yi kwace ko amsa ma a ce ƙarfin ya ci, amma ba kisa ko ɗauka a ce sai an kawo kuɗin fansa ba.
ABIN DA YA KAMATA DA SULHUN KATSINA
Bayan ɗaukar lokaci sulhun na tafiya cikin nasara, kamata ya yi Gwamnatin Tarayya da ta jiha, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da masu ilmi da manazarta su shiga maganar a ga yadda za a inganta shi, a kuma ƙarfafa shi ya zama abin koyi a ƙasar baki ɗaya.
Da an ɗauke shi a matsayin misali, aka bi hanyoyin ƙarfafa shi, tabbas da ya ƙara inganci. Amma yanzu wani wuri yana tafiya, wani wurin yana ɗigirgire.
ABIN DA ZA A TUNA DIKKO RAƊƊA DA SHI
Tarihi zai riƙa tuna Dikko Raɗɗa a matsayin Gwamnan da ya amshi mulkin Katsina cikin fushin halin rashin tsaron da jihar ke ciki. Amma bayan hawansa, ya gane cewa a kan tsaro sai dai ya yi abin da zai iya. Amma in ba da tallafin Gwamnatin Tarayya ba, ba zai iya samun nasarar da yake so ba.
Ya yi abin da zai iya, har da tallafa wa jami’an tsaro, da ɗaukar dakarun al’umma, da wayar da kan jama’a, da kuma amincewa da sulhun al’umma.
Har aka samu lokacin da aka ɗauki shekara ko fiye da haka ba kisa, ba korawa, ba kuma biyan kuɗin fansa a faɗin Katsina.