RA’AYI RIGA: Wa Zai Iya Ja Da Dikko Raɗɗa A Jam’iyyar ADC?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02042026_090152_FB_IMG_1775120104437.jpg

Muhammad Ahmed
@ Katsina Times

Ana ta muhawara a tsakanin manazarta kan zaɓen gwamnan Katsina mai zuwa a 2027. Sabuwar jam’iyyar ADC na ci gaba da samun tagomashi a faɗin ƙasar nan, har da jihar Katsina.

Wasu kujerun da za a yi takara a kansu, kamar na ’yan majalisun jiha da na tarayya, da kuma sanatoci, ana ganin za su iya zama “allura ce cikin ruwa, mai rabo ka ɗauka.”

Duk jam’iyyar da ta tsayar da ɗan takara na kirki, kuma ta tsare ƙuri’unta, ta kuma yi aiki sosai, za ta iya samun nasara -ko wace ce kuwa.

Zaɓen 2027, manazarta na ganin zai zama na daban, kuma wataƙila ya fi na 2015 sammatsi.

Mutane nagari sun fito a kusan kowace jam’iyya suna neman kujeru daban-daban. Lallai idan suka yi aiki kuma suka tsare ƙuri'unsu, za a iya samun “wake da shinkafa da miyar ja” a sakamakon sa.

ZAƁEN GWAMNAN KATSINA

Inda gizo ke saƙa shi ne zaɓen gwamnan Katsina! Wa zai iya karawa da Dikko Raɗɗa a ADC?

Abin da ya sa na ambaci Dikko Raɗɗa shi ne domin a fahimci cewa, a zaɓen 2027, mutum ne za a zaɓa, ba jam’iyya ba.

Sunayen mutane huɗu na yawo a jam’iyyar ADC a matsayin masu neman takarar gwamnan Katsina. Dukkaninsu mutane ne masu mutunci, kuma an san suna da kishin ci gaban Katsina. Amma…

1. SANATA ABUBAKAR SADIQ YAR’ADUA

Ya fito daga ƙaramar hukumar Katsina ne. Tsohon malamin makaranta, ƙwararren ɗan jarida, wanda har ya riƙe kakakin watsa labarai na gwamnan soja, tsohon ɗan Majalisar Tarayya, tsohon Sanata, kuma tsohon shugaban ma’aikata na fadar Kakakin Majalisar Ƙasa. Gogaggen ɗan siyasa ne.

Sadiq mutum ne mai son bin ƙa’ida da tsayawa kan tsari. Wannan na daga cikin dalilin da ka iya hana ADC ta ba shi takara.

2. SANATA AHMED BABBA KAITA

Daga ƙaramar hukumar Kankia. Tsohon ɗan Majalisar Tarayya ne, sannan tsohon Sanata. Ɗan kasuwa ne da ya tsunduma cikin harkokin siyasa. Ya yi aiki a lokacin da yake kan kujerar Majalisar Tarayya da kuma Sanata.

Ahmed Babba mutum ne tsayayye, amma wani lokaci bakinsa ba shi da linzami. Wannan na iya zama ƙalubale wajen ba shi tikitin Gwamna.

3. DAKTA MUSTAPHA INUWA

Daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa. Tsohon malamin Jami’a ne, tsohon Kwamishina, kuma tsohon Sakataren Gwamnati. A yanzu ana masa kirari da madugun adawar jihar Katsina.
Gogaggen ɗan siyasa ne, kuma ya fi na farko da na biyu daɗewa a siyasa. Mutanen na masa kallon sakainar ce iya ruwa. Sai dai wasu na ganin rashin ƙarfi a fannin kuɗi na daga cikin abin da ka iya hana shi samun takara.

4. LAWAL DAURA

Tsohon jami’in tsaro na DSS ne, wanda ya kai matsayin shugaban Hukumar a ƙasa. Sabon shiga ne a siyasa, ko kuma in ce sabon yankan rake ne.

Idan ya fito takara, har wasu daga cikin ’yan ADC na cewa gara Dikko Raɗɗa da shi.

Idan ka cire waɗannan huɗu, duk wanda aka kawo a ADC domin ya fafata da Dikko Raɗɗa, sai an yi masa gagarumin aiki na tallatawa kafin jama’a su karɓe shi -wanda hakan zai iya zama ƙalubale wajen cin zaɓe.

DIKKO RAƊƊA DA TAKARARSA

Ya karɓi mulki a 2023 a matsayin sabon shiga. A idon talaka, yana aiwatar da ayyukan da suke gani a ƙasa, waɗanda za su amfanar da su har ma da ’ya’yansu.

Tambayar 'ya ake aikin, nawa aka kashe? Wannan lissafi ne na masu ilimin boko wanda wani lokaci talaka ba ya fahimta. Idan ma ka yi masa bayani, zai iya cewa: “Duk wayon a ci ne, an kori kare daga gindin ɗinya.”

Ayyukan da ake gani a ƙasa, ba labari ba ne, na Dikko Radda, na nuna cewa jam’iyyar ADC na buƙatar ɗan takarar da zai iya gogayya da karon hatta da wannan ƙarfin.

Mafi yawan matsin tattalin arziƙin da ake ciki ba daga gwamnatin jiha ba ne, illa sakamakon wasu tsare-tsaren gwamnatin tarayya, waɗanda ke shafar ƙasar baki ɗaya.

A taƙaice, da alamu takarar gwamnan Katsina na iya zama bugun tazara ko kuma “free kick” ga Dikko Raɗɗa, amma sauran kujeru za su dogara ne da wanda aka tsayar.
Domin kuwa, ga dukkan alamu, a zaɓen 2027 mutum za a zaɓa, ba jam’iyya ba.

Muhammad Ahmad
Daya ne daga masu sharhi a jaridun katsina times ana iya samunsa a 08057777762
Katsina times
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar Taskar labarai @ Facebook page
Katsina city news @ Facebook page.
All social media handles. @ katsina times 
07043777779( whazzapp/ call)

Follow Us