KatsinaTimes
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekara 20 bisa zargin yunkurin kashe wani yaro dan shekara 10 a wani lamari da ake zargin yana da nasaba da tsafi.
Majiyoyin ’yan sanda sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Fabrairu da misalin karfe 7:30 na yamma a kauyen Kuidawa. Wanda ake zargin, mai suna Aliyu Ashabu, wanda ake kira da “Boka” a unguwarsu, an yi zargin ya yaudari yaron mai suna Alhassan Usman zuwa cikin wani daji da ke kusa, inda ya tura shi cikin wata rijiya.
An ceto yaron ne a ranar 23 ga Fabrairu ta hannun wani mutum sannan aka garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Katsina domin kula da lafiyarsa sakamakon raunukan da ya samu.
Binciken da jami’an ’yan sanda suka gudanar ya kai ga gano tare da kama wanda ake zargin. A yayin tambayoyi, an ce ya amsa laifin, inda ya bayyana cewa yana hada wasu tsafe-tsafe ne domin wani mutum mai suna Khalid, wanda har yanzu bai shiga hannu ba.
Rundunar ’yan sandan ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bisa zargin yunkurin kisan kai, aikata tsafi da kuma harkokin kungiyar asiri. Ana kuma ci gaba da kokarin cafke wanda ake zargin na biyu don fuskantar Shari'a.