TURJI YA SAKO LANKAI OFISA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02022026_223523_FB_IMG_1770071675199.jpg


Jaridun Katsina Times sun samu tabbaci cewa shahararren ɗan ta’adda Bello Turji ya saki ɗan bindigar yankin Jibia, Lankai, bayan kammala sasanci a tsakaninsu.

Majiyoyi daban-daban sun shaida wa Katsina Times cewa a halin yanzu Lankai yana hannun mutanensa, inda yake karɓar magani tare da duba lafiyarsa.

Wata majiya ta Katsina Times ta bayyana cewa ana zargin kuɗi sun shiga tsakani, domin biyan wani ramko da mutanen da suka yi garkuwa da Lankai ke ikirarin sun yi asara a lokacin rikicin.

Za a iya tunawa cewa a ƙarshen makon da ya gabata ne aka samu mummunan rikici tsakanin wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin mutanen Lankai. Lamarin ya sa aka yi hasashen cewa shima Lankai ya rasa ransa.

Sai dai daga bisani Bello Turji ya fitar da wani jawabi inda ya tabbatar da cewa Lankai yana da rai kuma yana hannunsa, yana mai cewa zai gudanar da bincike a kansa kafin ɗaukar mataki na gaba. A yau ne dai Turji ya sanar da sakin Lankai.

Katsina Times
www.katsinatimes.com

Follow Us