HATTARA!!! BARNAR BARAYI MASU HAYA DA BABUR YANA KARA MUNI A BIRNIN KATSINA.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22012026_111226_WhatsApp-Image-2022-06-01-at-4.31.30-PM.jpeg

Daga Muazu Hassan | 
Katsina Times Facebook page: Katsina City News 

Wani mummunan lamari da yake kara muni,a cikin katsina, shine ayyukan  barayi masu haya da babur, wadanda ke daukar mutane zuwa tashoshin mota da asuba, domin yin sammako zuwa wasu garuruwa.

Barayin na amfani da dubaru kala kala in sun dauko fasinja dubarar  farko itace, in sun lura inda suke ba mutane, sai suyi kamar  mashin din ya mutu sai suce fasinjan ya dan sauka.yana sauka zasu fisgi babur su gudu da kayan fasinjan.

Jaridun katsina Times sun samu irin wannan rahotannin a wurare da yawa  a cikin birni katsina. Na baya bayan nan shine wanda ya faru a yau alhamis 22/1/2026.wata mata da "ya "yanta uku tayi tafiyar dare daga garin Adamawa inda take aure.Matar tana dauke da kaya, niki niki har da buhun shinkafa da zata kaima uwayen ta.

Matar wani gari ce a karamar hukumar safana an sauke ta ne  a tashar Ktsa,da misalin karfe 6 na safe ta nemi dan Mashin ya kaita tashar ktsa dake filin ATC a kofar kwaya.Suna gaf da kwanar shiga tashar,sai  ya kashe mashin din yace, ta sauka ya gyara.Tana sauka ya fisgi mashin din da kayan ta,nan aka biyo ana ihu amma da yake jama a basu fara yawa ba.ya tsere.

Masu babura dake da wannan mummunar aika aikan sun fi aikin nasu a titunan yahaya madaki ,wanda ya taso tun daga kwanar tsohuwar central Bank zuwa tashar ktsa dake titin zuwa Batsari. 
Da wasu hanyoyin da suka tabbatar kafa bata fara zirga zirga da wuri.

Jaridun katsina times sun samu labarin faruwar wannan lamarin a gadar kofar kaura da kuma sama da kasan gadar kofar kwaya.
Jaridun katsina times sun samu labarin..masu wannan barnar sun fi fakar masu tafiya tun da safe kuma suna da kaya a tare dasu.

Jaridun katsina times sun gano hanyoyin da miyagun ke amfani dashi na tsayar da baburansu don su gudu da kayan mutum suna da yawan gaske.sai dai kawai kiyayewar Allah.
Yana da kyau mutane su fara hattara da rika hawan baburan da suka sani don tafiyar sassafe,in kuma ka iso tasha da dare ko asuba kayi hakuri gari ya waye kafin ka dau dan Babur ko kurkura.inji wani masanin tsaro 
Jaridun katsina Times sun yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun "yan sanda,amma bai dauki waya ba.

Katsina Times 
@ www.katsinatimes.com 
Facebook page; katsina city news 
Facebook page: jaridar taskar labarai 
All social media handles. Katsina times

Follow Us