Za A Saki Wasu Ɓarayin Daji Domin Zaman Lafiya Ya Ɗore A Katsina?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11012026_074454_FB_IMG_1768116987363.jpg



...Su waye? Me suka Aikata?

Daga Wakilanmu
Katsina Times

Jaridar Sahara Reporters ta wallafa wani rahoto a shafinta a ranar Alhamis 8/1/2025, wanda ya ginu a kan wata takarda da jaridar ta ce ta samu daga Ma’aikatar Shari’a ta jihar Katsina, wadda aka aike wa Babban Jojin Jihar Katsina.

A cewar Sahara Reporters, wasiƙar na neman Babban Jojin jihar da ya ba da haɗin kai domin sakin wasu daga cikin ɓarayin daji da ke tsare a gidajen yari na jihar Katsina, inda suke jiran shari’a. 

Rahoton ya nuna cewa sakin waɗannan mutane na daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da wasu ƙananan hukumomin jihar suka ƙulla da ɓarayin dajin.

Jaridar Katsina Times ta zurfafa bincike kan wannan takarda, inda ta tabbatar da inganci da sahihancinta. 

Binciken ya nuna cewa an rubuta wasiƙar a hukumance, kuma an tura ta ga Babban Jojin jihar Katsina, tare da bayyana buƙatar da ake nema a ciki.

Katsina Times ta kuma samu sunayen wasu daga cikin mutanen da ake neman a saki, ciki har da mace guda ɗaya, matasa 16 da kuma dattawa huɗu. 

Takardar ta bayyana shekarun kowanne, dalilan da suka sa aka tsare su, da kuma yankunan da aka kama su.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, Katsina Times ba ta samu tabbacin ko an fara aiwatar da shirin sakin waɗannan mutanen ba.

Tun bayan fitowar rahoton Sahara Reporters, masana shari’a da tsaro ke ci gaba da muhawara a shafukan sada zumunta dangane da lamarin. 

Haka kuma, wasu manema labarai na ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan wannan batu.
Wata tambaya da masana keyi, shine me yasa kwamishinar shari a, batayi amfani da ikon ta ba,na babbar mai shigar da kara ta jaha wajen sakin wadanda ake son a saka..sai ta amfani da babbar kotun jaha? 

Buƙatar Ɓarayin Daji Lokacin Sulhu

A yawancin zaman sulhu da ake yi da ɓarayin daji a ƙananan hukumomin da abin ya shafa, ɗaya daga cikin manyan buƙatunsu ita ce a saki ‘yan'uwansu da aka kama. Wannan buƙata kusan ita ce ta farko da suke jaddadawa a duk wani zama.

Sauran buƙatun sun haɗa da a ƙyale su su noma da kiwo ba tare da tsangwama ba, kuma a ƙyale su su sakata su wala, tare da kai musu kayan more rayuwa zuwa yankunan su. 

A wasu yankuna, kamar Ƙanƙara, an samu rahoton buƙatar rushe wani sansanin soji da ke yankin Mabai a matsayin wani ɓangare na shawarwarin sulhun.
Jaridun katsina times sun lura sulhun na tafiya cikin nasara a  mafi yawan kananan hukumomin da aka yi su.kuma barayin dajin sun saki kusan duk wadanda suka sace a hannun su domin neman kudin fansa..in banda na wasu yankuna kalilan.

Katsina Times 
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar Taskar labarai 
Facebook page: katsina city news 
Katsina Times All social media handles 
07043777779

Follow Us