Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 26 Disamba 2025
Injiniya Abubakar Abbati Muhammad, mazaunin Unguwar Alkali a Katsina, shi ne Shugaban Kungiyar Masu Gyaran Motoci ta Ƙasa (NATA) reshen Jihar Katsina. A wannan tattaunawa ta musamman da Katsina Times, ya yi bayani kan tarihin ƙungiyar, rawar da take takawa wajen horas da matasa, haɗin gwiwarta da gwamnatin Jihar Katsina, da kuma manyan ƙalubalen da ke fuskantar koyon sana’o’i a Najeriya.
A cewarsa, an kafa ƙungiyar NATA sama da shekaru 80 da suka gabata, kuma tana daga cikin tsofaffin ƙungiyoyin sana’a a Najeriya. Ya bayyana cewa ƙungiyar tana da tsari mai ƙarfi daga matakin ƙasa zuwa ƙasa, inda take da rassa a matakin unguwa, ƙaramar hukuma, jiha, har zuwa shugabanci na ƙasa.
“Ƙungiyar ta tattaro dukkan nau’o’in masu sana’ar gyaran motoci da injuna,” in ji shi. “Hakan ya haɗa da masu gyaran manyan motoci da ƙananan motoci, mashina da kekuna, masu faci, masu tada komaɗa (panel beaters), masu fentin motoci, da sauran masu alaƙa da harkar motoci.”
Injiniya Abbati ya bayyana cewa babbar nasarar da ƙungiyar NATA ta cimma a Jihar Katsina a shekarar 2025 ita ce shirin horas da matasa da aka aiwatar tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar.
“Babban abin da muka fi alfahari da shi a wannan shekara shi ne horas da matasa,” in ji shi. “Mun kulla yarjejeniya da gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta hannun Hukumar Katsina State Enterprise Development Agency (KASEDA), domin horas da matasa 3,000 a fannonin sana’o’in NATA.”
Ya ce a wannan tsari, NATA ce ke bayar da horo na sana’a, yayin da gwamnatin jihar ke biyan alawus da kuma tallafin kayan aiki ga masu amfana.
“A shekarar da muke bankwana da ita, mun samu damar horas da matasa 1,500,” in ji shi. “Mun bi tsari mai tsauri na tantance waɗanda za su ci gajiyar shirin, ta hannun shugabannin al’umma da hukumomin da suka dace, domin tabbatar da adalci da gaskiya.”
Injiniya Abbati ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kashe jimillar kuɗi Naira miliyan 74 wajen biyan alawus ga matasa 1,500 da suka halarci horon.
Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar na sa ran gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa waɗanda aka horas domin su kafa kansu da kansu.
“Muna fatan kowane wanda ya samu horo zai samu tallafin fara sana’a da ba zai gaza Naira dubu 400 zuwa dubu 450 ba,” in ji shi. “Wannan zai taimaka matuƙa wajen kafa su da kuma samar da abin dogaro. Muna yaba wa Gwamna Malam Dikko Umar Radda bisa wannan gagarumin ƙoƙari.”
Ya jaddada cewa koyon sana’a na ba matasa damar samun kuɗi cikin sauri fiye da wasu hanyoyin aiki.
“Idan an horar da matashi na tsawon shekaru biyu yadda ya kamata, zai iya samun aƙalla Naira dubu 5 a rana,” in ji shi. “Wannan yana nufin kusan Naira dubu 150 a wata. A wane mataki ne aikin gwamnati zai kai mutum wannan albashi cikin ɗan lokaci?”
Injiniya Abbati ya bayyana cewa NATA na ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa da hukumomi da kamfanoni na ƙasa da masu zaman kansu.
“Muna aiki tare da hukumomi kamar National Automotive Design and Development Council (NADDC), AMASCO, da wasu kamfanoni,” in ji shi. “Haka kuma, mun samar da wani tsari da zai taimaka wa jami’an tsaro, ya sauƙaƙa aikin hukumomin haraji, tare da kare martaba da mutuncin mambobinmu.”
Duk da nasarorin da aka samu, Shugaban NATA reshen Katsina ya bayyana cewa rashin cikakken goyon bayan iyaye maza na daga cikin manyan ƙalubalen koyon sana’a.
“Gaskiya, daya daga cikin manyan ƙalubalenmu shi ne yadda iyaye mata ke fi nuna kulawa wajen barin yara su koyi sana’a, yayin da iyaye maza da dama ba sa nuna irin wannan kulawa,” in ji shi. “Ya kamata iyaye maza su ƙara sanya ido da ƙarfafa ‘ya’yansu wajen koyon sana’o’i.”
Ya ce idan aka ba matashi kulawa da ƙarfafawa, cikin shekaru biyu zai iya zama ƙwararren mai sana’a mai dogaro da kansa.
Injiniya Abbati ya tabbatar da aniyar NATA ta ci gaba da ba da gudummawa wajen bunƙasa matasa, ƙwarewa, da tattalin arzikin Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya, tare da kira ga gwamnati da al’umma su ƙara haɗa kai.
Akwai cikakkiyar Tattaunawar ta bidiyo da zamu kawo maku a shafukan mu na facebook, YouTube, da sauran kafafen mu na sada zumunta