Fiye da gidajen Burodi 60,000 ne Suka Rufe a cikin Shekaru 4 – PBAN

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14112025_215755_FB_IMG_1763157454870.jpg



katsina Times

Shugaban Kungiyar Masu burodi ta Najeriya (Premium Breadmakers Association of Nigeria  PBAN), Injiniya Onuorah Emmanuel, ya bayyana damuwa kan tabarbarewar yanayin tattalin arziki da ke durkusar da masana’antar burodi a ƙasar.

Emmanuel ya ce fiye da rabin gidajen burodi na mambobin ƙungiyar sun daina aiki cikin ’yan shekarun nan, sakamakon tsadar kayayyakin aiki, hauhawar kudaden ruwa, da matsalolin tsaro da ke addabar sassan ƙasar.

Da yake jawabi a taron PBAN Day Out 2025 da aka gudanar a Legas, mai taken: The Business of Baking: Pathways to Profit, Productivity and Growth, Emmanuel ya bayyana matsanancin halin da ake ciki, yana mai cewa masu sana'ar burodi na fama da matsaloli masu yawa da ke barazana ga kasuwancinsu da kuma dubban ma’aikatansu.

Ya ce bayan barkewar cutar COVID-19, masu shagunan burodi da dama sun kasa farfaɗowa saboda tsadar kayayyakin aiki da rashin samun rance mai rahusa daga bankuna.

A cewarsa, rancen bankuna da ake samu yanzu suna kan kason fiye da kashi 30 cikin 100, wanda ya sa kasuwanci ke tangaltangal. “Kudaden rance suna danniya. Ba za ka iya samun rance mai ƙarancin ruwa daga banki ba. Ta yaya kasuwanci zai tsira da irin wannan tsada?” in ji shi.

Shugaban PBAN ya kara da cewa masana’antar  ta gidajen burodi ta shiga mawuyacin hali tun bayan annobar COVID-19. Ya ce daga cikin gidajen burodi sama da 140,000 da suka kasance suna aiki kafin shekarar 2020, yanzu ƙasa da 60,000 ne kawai ke ci gaba da aiki.

“Wannan ba matsalar masu burodi kaɗai ba ce. Halin durkushewa ya shafi kusan dukkan sassan masana’antu a Najeriya. Tsadar yin kasuwanci ta zama abin da ba za a jure ba,” in ji Emmanuel.

Follow Us