Shugaban kungiyar wayar da kan matasan karamar hukumar Batsari, watau Batsari Youth Public Enlightenment Forum a turance, kwamared Bello Lawal yayi kira ga gwamnatin jahar Katsina kalkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda Ph.D da masaurautar Katsina da su taimaka su nada Alhaji Sani Tukur Muazu Ruma sabon sarkin Ruman Katsina, hakimin Batsari.
Mr. Bello yayi wannan ikirari ne a yayin zantawar shi da wakilin mu, jim kadan bayan kungiyar ta kammala wani zama na musammun a ranar laraba 29-10-2025, a unguwar tashar Ruma dake Batsari hedikwatar karamar hukumar Batsari jahar Katsina, inda ya kara da cewa.
"Ina kira ga Mai girma gwamna Malam dikko umar raddah Phd da Ubanmu Uban kasa mai martaba Sarkin Katsina Alh. Abdulmuminu Kabir Usman da Dan majalisarmu na jaha Hon. Mustapha Tukur Ruma, da Kuma shugaban karamar hukumar Batsari Alh Mannir Muazu Rumah, suyi ma Alh. Sani Tukur Muazu Ruma (Sani mai Polo), Sarkin Ruman katsina hakimin Batsari wanda shine babban da ga Sarkin Rumah Kuma shine ke tafiyar da masarautar kafin rasuwar shi, lokacin da yake jinya. Yana da kyakkyawar alaka da mutanen Batsari halinsa halin mariganyi, watau mahaifin shi.
Don haka ne nake kira ga shugabannin namu da suyi mashi Sarkin Rumah don cigaba daga inda marigayi ya tsaya"
Dama dai a al'adar kasar Hausa, idan Allah yayi ma sarki cikawa, akan dauko babban dan sarki, a ba shi sarauta.