SULHU DA FULANIN DAJI DARASIN RIKIƊEWAR ƘUNGIYAR TSAGERUN YARBAWA TA OPC ...Daga Ganau

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes15102025_063950_IMG-20251015-WA0008.jpg



Daga Ɗanjuma Ƙatsina 

Tarihin Nijeriya daga 1993-1999 yana cike da darussa masu yawa. Marubucin nan shaida ne ga wasu waɗansu ma sunayensu sun fito a wasu muƙaloli da littattafan da aka rubuta.

Hawan Abacha kan mulki da neman miƙe ƙafa da ƙoƙarin cire kaki domin tabbata kan karaga ya haifar da ƙungiyoyin neman korar soja da ƙiyayya ga mulkin Abacha ta ɓangarori daban-daban.

Legas ce ta zama cibiyar gwagwarmaya a ƙasar nan. Kaduna da Kano nan ake tsara wasu shirye-shirye da suka shafi adawa da soja na arewacin ƙasar nan.

An kafa ƙungiyar kare muradun Yarbawa zalla mai suna OPC a shekarar 1993, wani Likita mai suna Frederick Fasehun shi ne ya kafa ta. Ya nemi matasa da suka fito daga tsatson talakawa su zama jigonta daga cikin su wani kafinta mai suna Gani Adams shi ya fi kowa ƙwazo.

A tsakanin lokacin a Legas akwai ƙungiyoyin neman kawo dimokariɗiyya sun kai 20, irin su Campaign for Democracy (CD) ta Dakta Beko Ransome-Kuti mafi yawan ƙungiyoyin sun yi ƙoƙarin samun wakilai a Arewa.

A 1997 ƙungiyoyin suka haɗu da neman kafa Majalisa ɗaya mai suna Revolutionary Council of Nigeria marubucin nan na wajen taron da aka yi ƙoƙarin kafa wannan Majalisar da ma wasu tarurrrukan da suka biyo baya.

Majalisa ce da ke da goyon bayan manyan attajiran Legas da ke gudun hijira da kuma wasu ƙasashen Yamma masu son ganin bayan mulkin soja.

Iyayen wannan Majalisar suka tsara za a fara fitar da 'yan Majalisar zuwa ƙasar Ghana domin koya masu yadda ake tada ƙayar baya a cikin manyan birane da yadda za a mayar da ƙasar mai zafi ga mulkin soja.

Kashin farko da suka fara tafiyar duk Yarbawa ne, kuma waɗanda suka fito daga ƙungiyar OPC.

Kashin farko sun dawo kafin a tura kashi na biyu sai Abacha ya mutu.

Salon tsarin da Abdulsalam Abubakar da ya gaji Abacha, ya zo da shi na mayar da mulki hannu farar hula da ƙoƙarin lallashin kowa ya wargaza Majalisar Revolutionary Council of Nigeria. 

Kungiyoyin daban-daban sun narke. An yi zaɓen da babu kamar sa. Har yanzu, jihohin Yarbawa jam'iyyar AD ta yi nasara wadda mafi yawan tsaffin 'yan gwagwarmayar dimokaridiyya ne har da babban madugu a cikinsu Tinubu da ya zama Gwamnan Legas a lokacin. 

An yi zargin gwamnatin Legas ta lokacin ta tattara waɗannan 'yan gwagwarmayar Yarbawan zuwa ƙungiyar OPC, inda suka riƙa ƙalubalantar komai na gwamnatin Tarayya da buga dundufar ƙabilanci.

'Yan OPC a wancan lokacin sun so mai da Nijeriya rana zafi inuwa ƙuna da ayyukansu da suke a Legas ƙarƙashin Gani Adams.

A shekarar 2000 Sufejo-Janar na 'yan sanda na ƙasa na wancan lokacin mai suna Musiliu Adeola Smith ya shelanta shugaban OPC na ƙasa a matsayin wanda ake nema da rai ko gawarsa, tare da sanya ladan Naira dubu dari ga duk wanda ya taimaka aka kama shi. 

Ya shiga hannu bayan wani lokaci. An kai shi kotu, kuma an sake shi.

Bayan sakin sa ne sai ya canza alƙiblar OPC zuwa mai kare muradin Yarbawa da muradinsu da kuma zama wata ƙungiyar 'yan sa-kai masu yaƙi da bata-gari.

Tabbas OPC ta yi sanadin kisa da mutuwar 'yan Arewa masu tarin yawa a yankin Yarbawa na ƙasar nan kuma a lokacin su suna da makamai muggai a wajensu.

A 2017 aka naɗa Ganiyu Adams a matsayin Sarkin yaƙin Yarbawa a taron gyaran tsarin mulkin da aka yi na shekarar 2005.

Gani Adams na cikin wakilan da aka turo daga jihar Legas. 

A shekarar 2018 na ziyarci Gani Adams a gidansa da ke Legas domin jin ta bakinsa a kan aiki wani littafin da nake mai suna Democracy in Nigeria; The Forgotten Heroes, wanda a ciki na kawo yadda aka manta da gudunmuwar da wasu 'yan Arewa suka ba da.

A gidansa ana ba shi tsaro kamar wani tsohon shugaban ƙasa. Na kuma taɓa ƙoƙarin magana da shi a Abuja, tsaro da tsare-tsaren da ake bi kafin a gan shi dole na haƙura.

Jami'an tsaron shi da kuma wanda gwamnati ta ba shi ke kula da shi.

Ɗan ta'adda yana iya canzawa, kuma ya sauya tsarin tafiyar da rayuwarsa, amma abin da na fahimta daga Gani Adams sai ilmatarwa da wayar da kai da cakuɗeɗeniya ya shigo sosai. 

Lokacin da Gani Adams ya kafa OPC, Sakandare kawai ya gama. Daga baya ya shiga makaranta har ya yi digiri. 

FULANIN DAJI
Sulhu da Fulanin daji na iya ɗorewa idan ilmi, faɗakarwa, yarda da juna da fahimta ta ginu.

Idan shugabannin su ,suka yarda a shiga cikin kananan su a wayar masu da kai.idan akayi maganin asalin matsalar .in haka ta faru ko da da makamai a wajensu zai zama maras amfani.
Danjuma katsina shine mawallafin jaridun katsina times,katsina city news Da jaridar taskar labarai.
Ana iya samunsa a 07043777779.

Follow Us