Rashin Kula da Halin Rayuwa: "Daga" Riko Ward a Katsina, Ta Shafe Shekaru 14 Ba Wuta. ...Ba Malamai A Makaranta Ba Asibiti

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13102025_204549_FB_IMG_1760388282994.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Kimanin kilomita 18 kacal daga cikin Birnin Katsina, garin "Daga" a Mazabar Riko da ke Karamar Hukumar Jibiya, inda al’umma fiye da dubu 18 ke rayuwa a yankin (Community), wacce ta dade cikin duhu da kunci na ci gaban rayuwa, duk da cewa tana da wakilai daga matakin ƙaramar hukuma zuwa na jiha da tarayya.

Kamar sauran ko wane yankuna a Najeriya, "Daga" a Mazabar Riko tana da kansila, shugaban karamar hukuma, ɗan majalisar jiha, ɗan majalisar tarayya, da sanata, wadanda dukkansu nauyin al’umma ke rataye a wuyansu. Sai dai, rahoton Katsina Times ya gano cewa wannan al’umma ta kasance cikin halin kunci da sakacin gwamnati, ba tare da lafiya, ilimi, ko wutar lantarki ba.

Lokacin da wakilin Katsina Times ya kai ziyara zuwa Riko, abin da ya gani ya girgiza. Asibitin garin Daga ya zama kango. Rufin dukkanin dakunan asibitin ya buɗe, bango ya fashe, babu ruwa ko kofi guda a cikinta Mata masu juna biyu sukan je haihuwa da jakar ruwansu a hannu.

Rahoton ya gano cewa akalla mata hudu zuwa bakwai ke haihuwa a kowane wata a cikin wannan hali, inda akwai ma’aikacin lafiya guda ɗaya da ke aiki, tare da wasu ‘yan sa-kai biyu ko uku. Ma’aikacin lafiyar ya shaida mana cewa shekara guda ce ta rage masa ya yi ritaya.

“Wannan asibiti ya zama tamkar gidan iskokai,” in ji wani mazaunin garin. “Idan ka kamu da ciwo, sai ka shiga da bisimilla.

A bangaren ilimi kuwa, makarantar firamare ta "Daga" a Riko tana da dalibai fiye da dari biyar, amma malamai uku kacal ke koyarwa, dukansu masu aikin sa-kai ne. Duk da cewa an gina sababbin ajujuwa, wasu sun riga sun lalace bayan makonni biyu zuwa uku da kammalawa.

Malamin da muka tarar da shi a makarantar ya bayyana cewa shi ɗan TP ne, babu ma’aikaci na dindindin ko mai gadi, kuma karatu ba ya gudana a duk kwanakin mako. “Muna iya zuwa sau uku a mako, mu ne kuma muke koyar da dukkan darussa,” in ji shi.

Abin da yafi ban mamaki shi ne yadda garin ya shafe shekaru goma sha hudu (14) ba tare da wutar lantarki ba. Sandunan wuta sun zama ado kawai a cikin gari wayoyin wutar kuwa sun zama tamkar wurin shanya kaya.

Ko da yake Sanata Abdu Soja ya kai transformer (rumbun adana wuta), mazauna yankin sun ce bai taba yin aiki ba.

“Transformer ta zama tamkar kayan ado ne kawai,” in ji wani cikin bakin ciki ya bayyana. “Muna ganin ta amma bata taba haska mana gari ba.”

Al’ummar Riko sun yi tir da halin ko in Kula na wakilansu. Sun zargi ɗan majalisar jiha Mustapha Yusuf da shafe shekaru 12 yana ɗumama kujerarsa ba tare da aikin cigaba ko guda ba a mazabar ba.

Haka kuma sun tambayi ɗan majalisar tarayya Sada Solin Jibiya, duk da cewa sun yaba da gudunmawar da ya bayar ta kayan asibiti da suka kai darajar miliyoyin naira, amma kayan sun kasa amfani saboda lalacewar asibitin.

A gefe guda, sun soki Sanata Abdu Soja saboda transformer da ya kai bata aiki, da kuma Gwamna Dikko Umar Radda wanda aka karrama da Golden Award a Abuja saboda kokarinsa a fannin ilimi, amma makarantar firamare ta Daga a cikin Mazabar Rikon karamar hukumar Jibiya jihar Katsinan Dikko Radda tana fama da rashin malamai da lalacewar gine-gine.

Duk da kasancewarta kusa da Birnin Katsina, garin Daga da Riko sun zama tamkar yankin da aka manta da shi gaba ɗaya. Ba lafiya, ba ilimi, ba wuta babu wani abu da ya nuna romon dimokuraɗiyya.

“Mu muna kada kuri’a a kowane zabe,” in ji wani dattijo, “amma me muke gani? Ko fitilar da za mu ga kuri’ar mu ba mu da ita.”

Follow Us