Karamar Hukumar Katsina ta sake shirya taron addu’o’in neman zaman lafiya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05102025_181306_Screenshot_20251005-180641.jpg



Karamar Hukumar Katsina ta sake shirya taron addu’o’i da saukar Alƙur’ani mai tsarki domin neman zaman lafiya da albarka ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

Taron ya gudana ne a babban masallacin Juma’a na Muhammadu Dikko da ke Kofar Soro a cikin birnin Katsina, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Honarabul Isah Miqdad A.D. Saude.

A taron, shugaban ƙaramar hukumar wanda mataimakinsa Honarabul Yusuf Usman Saulawa ya wakilta, ya ce taron addu’o’i da karatun Alƙur’ani hanya ce tabbatacciya ta samun sauƙin matsalolin da ake fuskanta a jihar.

“Mun taru a wannan masallaci domin saukar Alƙur’ani da yin addu’a don neman albarka da sauƙin matsalolin da muke ciki. Ci gaba da yin addu’a da karatun Alƙur’ani shi ne mafita ga matsalolinmu,” in ji shi.

Ya ce matsalar tsaro a jihar tana raguwa sannu a hankali, inda ma wasu daga cikin masu aikata laifuka ke neman sulhu. Ya danganta hakan da tasirin addu’o’in malamai masu albarka.

A nasa jawabin, mai ba Gwamnan Katsina shawara kan harkokin Darika, ya yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa nuna muhimmanci ga malamai da shehunnai, yana mai cewar wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan taro bayan wanda aka fara yi a Masallacin sakatariyar ƙaramar hukumar.

 “Yanzu haka gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda tana ganin amfanin waɗannan addu’o’i a ko’ina cikin jihar. Makarantu da tsangayu na ci gaba da gudanar da irin wannan aiki domin tabbatar da zaman lafiya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar da ta ƙaramar hukumar Katsina na godiya ga malamai da shehunnai bisa jajircewarsu wajen ci gaba da yin addu’o’i don zaman lafiya.

Ya yi addu'ar cewar: “Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya a jiharmu da ƙasarmu. Wannan ƙasa da wannan jiha Allah ne ya kaddara mu rayu a cikinsu,” yana mai karkarewa da cewar jihar Katsina na samun farfaɗowa daga matsalar tsaro sakamakon ƙoƙarin da gwamnan jihar, Dikko Radda ke yi da kuma addu’o’in malamai.

Malamai da shehunnai da suka jagoranci addu’o’in sun haɗa da Khalifa Sheikh Ahmad Tijjani, babban halifan zawiyyar Tijjaniyya ta jihar Katsina, Sheikh Dayyabu Zanguna, Sheikh Usman Namadi, da Sheikh Malam Mustapha, babban limamin masallacin Juma’a na Katsina, da sauransu.

Hakazalaika, taron ya samu halartar wakilin Magajin Garin Katsina, S.A Darika, kansiloli, da dimbin jama’a daga sassa daban-daban na  karamar hukumar.

Follow Us