Kwalejin Gial ta Katsina ta yaye dalibai 100 karo na farko.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20092025_183844_FB_IMG_1758393479407.jpg

Auwal Isah | Katsina Times 

Kwalejin 'Gial College of Higher Education' da ke Katsina, wadda ke da haɗin gwiwa da Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), ta gudanar da bikin yaye dalibai 100 karo na farko tun bayan da aka kafa ta.

Bikin yaye daliban ya gudana ne a dakin taro na makarantar da ke Lambun Danlawan a ranar Asabar, inda malamai, iyaye, ‘yan'uwa da abokan arziki, da kuma manyan baƙi daga ABU suka halarta.

A jawabinsa, Magatakardar makarantar, Dr. Sirajo Aminu, ya bayyana cewar wannan biki ya zo daidai da cikar kwalejin shekaru biyu da fara gudanar da karatu. Ya kuma bayyana cewa nasarorin da makarantar ta samu ba su yiwu ba da b don ƙoƙarin wanda ya assasa makarantar ba, wato Hon. Hamisu Gambo (Danlawan Katsina).

"Mai girma Danlawan ya yi babban abin alheri. Lokacin da aka fara darussa, shi da kansa ya ɗauki dalibai 30 kyauta, ya ce a fara karatu. Duk kudin da ake kashewa shi ne yake bayarwa. Gaba ɗaya, kashi 85% na nasarorin makarantar daga farko zuwa yanzu daga gare shi suke.” in ji Dr. Sirajo.

Ya ƙara da cewa makarantar na ci gaba da ƙoƙari wajen samun amincewar hukumomi domin fara shirye-shiryen karatun digiri a fannoni daban-daban.

Haka zalika, wakilin Jami’ar ABU, Dr. Aliyu Sani Kiyawa, ya yaba da yadda makarantar ke tafiyar da tsarin karatu bisa ka’idojin da jami’ar ta gindaya, yana mai tabbatar da cewa ABU ta gamsu da ingancin ayyukanta.

A nasa jawabin, Hon. Hamisu Danlawan, wanda shi ne uba kuma ginshiƙin kwalejin, ya nuna farin cikinsa da haɗin gwiwar da suka samu daga ABU, wanda ya ba su damar koyar da kwasa-kwasan diploma a ƙarƙashin kulawar jami’ar.

"Yau dalibanmu 100 sun kammala kwasa-kwasan diploma daga ABU Zariya. Wannan babbar nasara ce a gare mu. Muna gode wa ABU da ma Hukumar 'Higher Education' ta Katsina bisa amincewa da wannan haɗin gwiwa,” in ji shi.

Danlawan, ya kuma gode wa mutanen da suka tallafa wajen ɗaukar nauyin wasu ɗalibai, yana mai jinjina wa Ambasada Yahaya Lawal, Hon. Yusuf Majigiri, da Hon. Sani Danlami a matsayin misalai.

Daga ƙarshe, Danlawan ya shawarci daliban da su yi amfani da ilimin da suka koya, tare da ci gaba da zurfafa karatunsu zuwa matakin gaba.

Daliban 100 da aka yaye sun fito ne daga sassa guda biyar da suka hada: Nazarin Kimiyya (Integrated Science), Ilimin Addinin Musulunci (Islamic Studies), Nazarin Harshen Turanci (English), Nazarin Harshen Hausa, da kuma Ilimin Maktaba (Library Studies).

Follow Us