Karamar hukumar Katsina Ta Fara Horaswa da Bada Tallafi Don Bunkasa Kananan Sana’o’i ga mutane 140, na Mazabar Wakilin Arewa "A"

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16092025_160852_FB_IMG_1758038863643.jpg

Katsina Times | Talata, 16 ga Agusta, 2025



Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD, ya kaddamar da shirin horas da ’yan kasuwa kanana 140 daga mazabar Arewa “A”, a birnin Katsina a haɗin gwiwa da Hukumar Bunkasa Matsakaitan da Kananan Sana’o’i ta Ƙasa (SMEDAN).

An gudanar da taron ne a dakin taro na sakatariyar ƙaramar hukumar ranar Talata 16 ga watan Satumba 2025, inda Hon. Miqdad ya bayyana cewa manufar shirin ita ce koyar da matasa da masu kananan sana’o’i dabarun inganta kasuwancinsu, tare da basu tallafin kuɗi bayan kammala horo.

“Mun shirya wannan shiri tare da SMEDAN domin ku samu dabarun bunkasa sana’o’inku. Bayan horon kuma za mu samar da tallafin kuɗi. Wannan shiri hujja ce ga ’yan adawa da ke cewa gwamnati bata baiwa kananan hukumomi haƙƙinsu ba. Gwamna Dikko Radda ya tabbatar da cewa kananan hukumomi suna samun cikakken ikon kashe kuɗinsu,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa SMEDAN bisa haɗin kai, tare da roƙon masu cin gajiyar shirin da su yi amfani da damar yadda ya kamata. Ya ce sauran mazabu za su biyo baya nan gaba kadan.

A nasa jawabin, Shugaban SMEDAN a Jihar Katsina, Alhaji Baffa, ya ce horon zai taimaka wajen fadada harkokin kasuwancin masu kananan sana’o’i, tare da samar da sabbin dabaru na kasuwanci.

Taron ya haɗa da gabatar da kasidu da tattaunawa da suka shafi hanyoyin bunkasa harkokin sana’o’i, tare da halartar maza da mata masu kananan sana’o’i daga mazabar Arewa “A”na cikin garin Katsina.

Follow Us