KatsinaTimes
Gwamnatin Tarayya ta amince da ware kudade kimanin Naira biliyan 1.85 domin ci gaba da ilimi, gyara da kuma zaman su cikin al’umma ’yan matan Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram.
Ma’aikatar Ilimi ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Folasade Boriowo, ta fitar a ranar Alhamis, inda ta ce shirin zai ɗora kan Shirin Gyara da Tallafa Wa ’Yan Matan Chibok har zuwa shekarar 2027.
Sanarwar ta ce tallafin zai haɗa da kuɗin makaranta, masauki, horaswa ta sana’o’i, tallafin kwantar da hankali, da sauran abubuwan jin daɗi ga waɗanda aka ceto da har yanzu ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa:
“Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ƙarƙashin tsarin Renewed Hope Agenda, na tabbatar da cewa waɗannan ’yan mata 108 da aka mika wa Ma’aikatar Harkokin Mata suna samun cikakken tallafi na ilimi da gyara domin inganta rayuwarsu.”
Ya ƙara da cewa, yanzu haka 68 daga cikin ’yan matan suna karatu a Jami’ar Amurka da ke Yola, mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kuma gwamnati za ta ci gaba da biyan kuɗin makaranta da masaukinsu duk da sukar da wasu ke yi game da tsadar shirin.
A cewar Ma’aikatar, wannan shiri ba wai na kuɗi kaɗai ba ne, illa ma wani nauyi ne na ɗabi’a da tarihi wajen tabbatar da makomar waɗannan yara:
“Wannan alƙawari ba kuɗi kaɗai ba ne, alƙawari ne na ɗabi’a da kuma tarihin ƙasa. Alƙawari ne na maida wannan babi na baƙin ciki cikin tarihinmu zuwa labarin juriya, mutunci da fata.”
A ranar 14 ga Afrilu, 2014 ne Boko Haram suka sace dalibai mata 276 daga Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Chibok, Jihar Borno.
Har yanzu ana ci gaba da neman 87 daga cikinsu, yayin da aka ceto ko aka sako 108 cikin lokaci daban-daban a cikin shekaru. Da dama daga cikin waɗanda aka ceto sun samu shirin gyara, kulawar lafiya, taimakon shawo kan ɗ trauma, da kuma tallafin ilimi.