Tawagar uwar jam'iyyar Apc ta jihar Katsina ta ziyarci katafariyar Hedikwatar jam'iyyar ta jiha da ake ginawa Katsina.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes01092025_215652_IMG-20250901-WA0329.jpg


A ranar litinin 01!/09/2025 Uwar jam'iyyar ta jihar Katsina karkashin jagorancin shugabanta na jiha Alh. Sani Aliyu JB Daura sukayi ziyarar gani da ido a sabuwar hedikwatar dake hanyar Dutsinma nan cikin garin Katsina. 

Da yake gabatar da jawabin sa bayan kammala ziyarar shugaban jamiyyar Apc na jihar Katsina Alh. Sani Aliyu JB ya fara da godiya ga Allah da ya nuna masu wannan rana tare da nuna jin dadin sa akan yadda sukaga wannan aiki.

Ya kuma yi godiya ga tsohon gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari wanda shine ya assasa wannan aiki tare da mika cikakkar godiyar su ga gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda Ph'D CON wanda yake cigaba da aikin a yanzu. 

Kuma yayi alkawalin kammala aikin kafin nan zuwa watan Satumba tare da yin duk abinda ya dace a ofishin wanda babu irin sa a duk fadin jihohin Arewa ko Najeriya ma baki daya.

A nasa jawabin Injiniyan dake kula da aikin Engr. Muntari Sagir Malumfashi  wanda ya samu wakilcin Engr. Faruk Sani ya bayyana cewa" zuwa yanzu wannan aiki ya kai kaso saba'in cikin dari kuma in sha Allah zasu kammalla wannan aiki zuwa watan Satumba.

Kuma wannan aiki kamfanin Muntasarab Global Ventures karkashin jagorancin Engr. Muntari Sagir Malumfashi ne ke gudanar shi.

Tawagar  da ta ziyarci hedikwatar ta kunshi dukkan masu mukaman jam'iyyar na jihar Katsina.

Follow Us