Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gaggauta magance matsalolin da suka dade suna damun jami’ar, tana mai gargaɗin cewa idan aka yi sakaci, jami’ar za ta shiga cikin mummunar matsala.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Murtala Kwara, ya bayyana a taron manema labarai ranar Litinin cewa akwai muhimman buƙatu guda huɗu da suka shafe fiye da shekaru biyu ba tare da gwamnatin ta ɗauki mataki ba.
1. Rikicin Tsarin Albashi
Dr. Kwara ya ce duk da cewa gwamnatin tarayya ta riga ta amince da sabon tsarin albashi ga jami’o’i, Jihar Katsina ta fito da wani tsarin da “ba na tarayya ba ne, kuma ba na tsohon tsarin jihar ba ne.”
“Mun tattauna da jami’an gwamnati, amma suka yi watsi da shawarar mu. Abin da muke nema shi ne a bi tsarin albashin da ake amfani da shi a jami’o’in tarayya,” in ji shi.
2. Cire Kuɗin Fansho Ba Tare da Bayani Ba
Shugaban ASUU ya kuma zargi gwamnati da cire kuɗin fansho daga albashin malamai na tsawon watanni tara, amma ba a ba su damar zaɓar masu kula da asusun fansho (PFA) ba kamar yadda doka ta tanada.
“Ana rika cire mana kuɗi, amma har yanzu ba mu san inda ake turawa ba. Wannan doka ta hana, kuma ba abin da za mu lamunta da shi ba ne,” ya ƙara da cewa.
3. Matsalar Kachima (Asusun Inshorar Lafiya)
Game da shirin inshorar lafiya na jihar, KACHIMA, Dr. Kwara ya ce shirin mai kyau ne a rubuce, amma ya gaza a aiwatarda tsarin yadda ya kamata
“’Yan uwa malamai ba sa samun kulawa daga cibiyoyin lafiya. An sha ce musu cewa hukumar Kachima tana biyan su ₦400 kacal a kan kowane mutum a wata. ₦400? Alhali kuwa ko paracetamol yanzu ya kai kusan ₦300. Ta yaya za a gudanar da lafiya da wannan kuɗi?” ya tambaya.
ASUU ta buƙaci gwamnati ta ƙara kuɗin da ake warewa ko kuma ta cika alƙawarin da ta ɗauka na ɗorawa a kan kuɗin da ake karɓa.
4. Barazanar Ƙwace ‘Yancin Gashin kan Jami’a
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan labarin da ke yawo cewa gwamnatin jihar na shirin miƙa aikin kula da bayanan jami’a ga wani kamfani mai suna Flexisub, wanda ƙungiyar ta ce ba shi da kwarewar da ake buƙata.
“Jami’a na da ‘yancin gashin kanta bisa dokar 2003. Sashen ICT na UMYU na da ƙwararru masu iya gudanar da bayanai da harkokin makaranta. Miƙa wannan aiki ga kamfani maras ƙarfi hatsari ne,” in ji shi.
Barazanar Yajin Aiki
ASUU ta bayyana cewa wannan matakin da ta ɗauka yanzu “matakin farko ne na rikicin ma’aikata,” amma ta yi gargadin cewa idan aka ci gaba da yin shiru, za ta shiga yajin aiki.
“Mun rubuta wa shugabanci, kwamitin gudanarwa, da ma Gwamna kansa. An kafa kwamiti watanni takwas da suka gabata don a duba matsalar albashi, amma har yanzu babu wani sakamako. Idan gwamnati ba ta yi gaggawa ba, mataki na gaba shi ne yajin aiki,” in ji Dr. Kwara.
Saƙo Kai Tsaye ga Gwamna Radda
A cikin jawabin sa na musamman, Dr. Kwara ya tunatar da Gwamna Dikko Umaru Radda—wanda shi ma mai digirin PhD ne—cikin girmamawa da damuwa cewa malamai da al’ummar jami’a na da babban fata a gare shi.
“Malamai abokan aikinka ne, suna kuka. Muna shirye mu ba da shawara, amma halin da jami’ar ke ciki na kara tabarbarewa. Muna roƙon ka ka sa baki domin ceton UMYU,” ya yi kira.
ASUU ta rufe taron da gargadi ga gwamnati cewa ci gaba da watsi da waɗannan matsaloli zai iya lalata ba kawai jami’ar ba, har ma da tsarin ilimi gaba ɗaya a Jihar Katsina.