Muazu Hassan @ Katsina Times
Wata kungiya mai suna katsina security community initiative zata gudanar da taro akan tsaro na masu ruwa da tsaki akan matsalar tsaro dake addabar jahar katsina.
Kungiyar wadda ke bisa jagorancin Dakta Bashir Usman kurfi da kuma sakataren ta Malam Abdullahi Hassan kofar sauri an kafa ta ne shekarun baya a katsina.
Taron wanda za a gudanar da shi a dakin taro na Munaj event center da karfe goma na ranar talata 2 ga watan satumba 2025.
Taron ya gayyato masu magana daban daban a ciki da wajen jahar katsina daga cikinsu akwai farfesa Usman yusufu yar adua,Dakta usman Bugaje,Dakta Abubakar Saddiq , Ambassador sani Bako, birgediya janar Isma'il Abdullahi mai ritaya.birgediya janar Maharazu tsiga.Hon Jamilu Mamman Dan musa.
Masu shirya taron sun ce..za a tattauna matsalar tsaro a katsina, inda ake ina kuma aka dosa?
A baya ita wannan kungiya tayi wani aikin tsaro tare da gwamnatin Masari inda ta rika aiwatar da wasu ayyukan karfafa yan sintiri gwaiwa da ilmantar da yankunan da tsaro ya addaba me zasuyi.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page: katsina city news
Jaridar Taskar labarai
All on All social media handles
07043777779.