Katsina Times Ta Bankado Halin Da Rabi Isma’il ‘Yar Kannywood Ke Ciki a Yanzu bayan hukuncin Kisa
Daga Mukhtar Yakubu da Mu’azu Hassan | Katsina Times
Shekaru 14 kenan da Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga tsohuwar jarumar Kannywood, Rabi Isma’il, wacce aka fi sani da Rabi Acid ko Rabi Sisiliya. Tun daga wancan lokaci take zaman jiran ranar da za a zartar da hukuncin a kanta.
A ranar 8 ga Yuli, 2011 ce Kotun Koli ta tabbatar mata hukuncin kisa, bayan shari’a mai tsawo daga kotun jiha, zuwa kotun daukaka kara har zuwa kolin shari’a a Abuja. Alkalan kotun bakwai karkashin Mai Shari’a Francis F. Tabai sun bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun isa wajen tabbatar da aikata laifin.
A ranar Kirsimeti ta shekarar 2002 ne, a wurin shakatawar Tiga da ke Karamar Hukumar Bebeji, Kano, Rabi ta tunkuda saurayinta, Alhaji Ibrahim Zazu, cikin ruwa, bayan ta ba shi alewa da aka ce ta gauraya da maganin bacci. Rahotanni sun ce bayan ya fita daga hayyacinsa, ta kwashe kudadensa sannan ta tura shi cikin ruwa har ya rasa ransa.
Babbar kotun Kano karkashin Mai Shari’a Halliru Muhammad Abdullahi ta fara yanke mata hukuncin kisa a ranar 5 ga Janairu, 2005. Daga nan ta daukaka kara, amma kotunan Kaduna da Abuja duk sun tabbatar da hukuncin.
Kamar labarin fim, a ranar 16 ga Disamba, 2011, Rabi ta tsere daga gidan yarin Hadejia bayan wani jami’in gidan yari da ake zargin ta yi soyayya da shi ya taimaka mata. Wannan tserewarta ta girgiza hukumomi, inda aka dora alhakin sakacin akan jami’in tare da rage masa mukami.
Sai dai a ranar 21 ga Mayu, 2017, jami’an tsaro na DSS tare da hadin gwiwar hukumar gidajen yari suka sake cafke ta a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin. Daga nan aka mika ta gidan kurkukun Kuje, kafin daga bisani a tura ta gidan yarin Kirikiri, Legas, inda take tsare yanzu haka.
Binciken Katsina Times ya gano cewa Rabi ta rungumi kaddara a gidan yari, inda take zaune a sashen masu jiran kisa. Majiyoyi daga cikin gidan yarin sun ce tana rayuwa ba tare da nadama ba, kuma har yanzu tana da saurin fushi da fada da duk wanda ya shiga gabanta.
An kuma tabbatar da cewa kafin tafiyarta gidan yari, Rabi ta riga ta haihu. A yanzu ’ya’yanta sun girma, suna aiki, kuma wani lokaci suna kai mata ziyara a Kirikiri.
Katsina Times ta samu sabon hoton Rabi daga ma’aikacin gidan yarin a wannan shekarar 2025. Hoton ya nuna ta yanzu da shekaru, amma har yanzu tana da kwalliya da son burgewa, duk kuwa da halin tsarewa da take ciki.
Katsina Times ta tabbatar da wannan bincike daga shaidu da suka tabbatar da kasancewarta a Kirikiri Prison, Legas, domin idan aka bar ta a wasu kurkuku, akwai fargabar ta sake tserewa kamar yadda ta taba yi a baya.
Katsina Times
www.katsinatimes.com
Social Media: Katsina Times | Katsina City News | Taskar Labarai
07043777779 | 08057777762