Gwajo-Gwajo Ya Bukaci Al'ummar Jihar Katsina Da Su Yi Rijistar Zabe

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23082025_000546_PVCs-1.png


Mai ba Gwamna Dikko Umar Radda shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, ya yi kira ga waɗanda suka isa yin rijistar katin zabe a jihar, da su shiga rijistar da hukumar zabe ta ke gudanarwa a fadin kasar nan.

A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Katsina, Alhaji Ya'u Gwajo-Gwajo ya bukaci 'yan jihar da suka cika shekaru 18 bayan an kammala rajistar zabe na shekarar 2022, da masu son canza rumfunan zabensu, da su shiga shafin yanar gizo na hukumar INEC domin yin rajista.

Ya bukaci al’ummar jihar da su bai wa gwamnatin jihar hadin kai a yunkurinta na ganin jihar Katsina ta cigaba da kasancewa cikin jihohin dake kan gaba wajen yawan masu rajistar zabe a fadin kasar nan.

“Muna da sama da mutane miliyan 3.5 da suka yi rajista, jihar Katsina ita ce ta biyar mafi yawan masu rajista a Najeriya, a bisa kididdigar karshe da aka fitar a shekarar 2023, ya kamata mu wuce haka, ko a kalla mu rike matsayinmu.

"A matsayinmu na jiha ta uku a yawan al'umma a Najeriya, ya kamata mu kasance jiha ta uku a yawan masu rajistar zabe a kasar, za mu iya cimma hakan ne kadai idan duk waɗanda suka kai shekaru 18 zuwa sama suka fito suka yi rajista".

Gwajo-Gwajo ya bayyana cewa, bisa ga bayanan hukumar INEC, a cikin kwanaki biyar kacal har mutane 505,000 sun yi rajista, yace hakan ya nuna muhimmancin da akasarin jihohi ke ba aikin rijistar.

“Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce sama da ‘yan kasa 505,906 ne suka yi rajista daga lokacin da aka fara rijistar a farkon makon nan.

“Wannan ya nuna aniyar INEC na inganta tsarin zabe da kuma gudanar da sahihin zabe, don haka bai kamata a bar al’ummar jihar Katsina a baya ba, duk wadanda suka cancanta su yi rijista, wajibi ne su yi rijista.

“Duk ‘yan asalin jihar da suka kai shekaru 18 zuwa sama, da masu son sabunta ko canza garin da suke zabe, su yi gaggawar yin amfani da wannan damar.

“Ya kamata masu rike da mukaman gwamnati, da kungiyoyin farar hula, da shuwagabannin al'umma, da kafafen yada labarai, da duk masu ruwa da tsaki su wayar da kan jama’a a kan muhimmancin yin rijistar zabe.

“An riga an fara yin rijistar ta yanar gizo, yayin da za a fara rajistar ta zahiri a mako mai zuwa a dukkan ofisoshin INEC na jihohi da na kananan hukumomin kasar nan.

“Wadanda suka riga suka yi rajista kada su sake yi, amma duk wadanda ba su yi ba ko kuma suke so su sabunta, ko su canza rumfunan zabensu, to su garzaya su je ofishin hukumar INEC mafi kusa da su sabunta rijitarsu,” in ji sanarwar.

Follow Us