Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 21 ga Agusta, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da horon saukakawa (Step-down Training) ga malamai 18,000 tare da rabon kwamfutar hannu 20,000 ga wasu daga cikinsu, domin ƙarfafa koyarwa da inganta ilimi a fadin jihar.
An gudanar da bikin a harabar Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi da ke kan titin Kaita, inda Mataimakin Gwamna Malam Faruq Lawal Jobe ya wakilci Gwamna Dikko Umar Radda.
A jawabin sa, Jobe ya bayyana wasu muhimman matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka wajen inganta ilimi. Ciki har da rabon kayan makaranta da unifom 30,000 ga yara marasa galihu, samar da kayan koyarwa na musamman ga makarantun makafi da kurame, da kuma sanya na’urorin CCTV a makarantu 130 domin tsaro. Haka kuma gwamnati ta raba babura 70 ga jami’an sa ido don inganta duba makarantu a ƙauyuka.
“Waɗannan ba wai kididdiga ba ne kawai, jarin makoma ne,” in ji shi. “Mun fara ɗora malamai kan tafarkin zamani ta hanyar basu kayan aiki da horo domin su koyar bisa ka’idojin duniya tare da shirya ɗalibanmu su iya fafatawa a ƙarni na 21.”
Koodinetan shirin TESS ta jihar, Hajiya Binta Abdulmumini, ta bayyana cewa wannan shiri na haɗin gwiwa da Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya zai horar da malamai 18,000 ta hannun kwararrun malamai 90 da aka horar a matakin farko. Kowanne malami zai samu kwamfutar hannu da aka loda da shirye-shiryen darussa da kayan sa ido na zamani.
Shugabar ƙungiyar malaman jihar Katsina, Hajiya Rakiya Shehu, ta yabawa gwamnatin jihar bisa kulawar da take nunawa ga malamai da ɗalibai tare da kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar an cimma nasarar shirin.
Ita ma Kwamishiniyar Ilimi na Firamare da Sakandire, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana wannan mataki a matsayin “muhimmin ci gaba” wajen dawo da martabar ilimi a jihar. Ta kuma gode wa Bankin Duniya, UBEC, da sauran abokan haɗin gwiwa bisa goyon bayansu.
Bikin ya samu halartar manyan baƙi da dama, ciki har da Babban Alkalin Jihar Katsina Mai Shari’a Musa Danladi, Shugaban SUBEB Dr. Kabir Magaji, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina, kwamishinoni da manyan shugabannin jami'an tsaron na jihar Katsina.