Auwal Isah Musa | KatsinaTimes
Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da wani Kwamitin hadin gwiwa na Masu Ruwa da Tsaki a Harkar Ilimi wanda zai daidaita harkokin ilimi a fadin jihar, wanda aka ambata da 'Joint Education Sector Coordination Committee' a turance.
Kwamishinar Ma'aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta jihar, Hajiya Zainab Musan Musawa, ce ta jagoranci taron kaddamarwar a dakin taro na ERS a ranar Talata.
Tun da farko, da take jawabi a wajen taron, Hajiya Zainab ta bayyana wasu muhimman nasarori da gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta samu a 6angaren ilimi, ciki har da: Gyaran makarantu sama da 150 da kuma gina sabbin makarantu a yankunan Katsina, Funtuwa da Daura, Daukar malaman makaranta sama da 7,000 tare da shirin daukar karin malamai don cike gibin wasu, Bunkasa ilimin 'ya'ya mata ta hanyar shirin AGILE, Bayar da tallafin karatu, da kuma shirye-shiryen horaswa na musamman, da kuma Shirye-shiryen zakulo basirar matasa kamar shirin “Catch Them Young”, wanda ake koya wa 'yanmata dabarun rayuwa da ilimin kwamfuta.
Sai dai, ta kuma bayyana wasu kalubale da bangaren ilimi ke fuskanta, wadanda suka hada da: Matsalar tsaro a wasu sassan jihar, Karancin malamai da muhallin koyarwa, Magudin jarabawa, Karancin kudade, Rashin tsayayyar manhajar karatu da sauransu.
Hajiya Zainab, ta yi kira ga kafatanin masu ruwa da tsaki a harkar ilimi; Iyaye, da shugabannin gargajiya da cewar su hada kai da gwamnati wajen samo karin hanyoyin ware-ware wadannan kalubale don inganta ilimin yaranmu, da tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari a baya.
"Maza da mata, ilimi shi ne ginshikin ci gaba. Makomar Jihar Katsina tana cikin jarin da muke zuba wa yau ga 'ya'yanmu. Muna bukatar hadin kanku da jajircewarku. Mu gina tsarin ilimi da ba zai bar wani yaro a baya ba." Ta yi kira.
A yayin taron, an bayyana manufofi, burin da ake so a cimmawa, da kuma yadda ake sa ran kwamitin zai gudanar da aikinsa don tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga yaran jihar, ba tare da an bar wanisu a baya ba.
Har wayau, kwamitin, ya tafi da nufin tabbatar da wadannan kudururruka: Ƙarfafawa da daidaita harkokin bangaren ilimi, tallafawa wajen bunkasa dabarun ilimin jihar, aiwatar da manyan abubuwan da aka fi so a mayar da hankali kansu a bangaren ilimi, zakulo gibi tare da bayar da shawarwarin don samun mafita da kuma taimaka wa juna wajen musayar bayanai a tsakani.
Wadanda suka halartarci taron kaddamar da kwamitin sun hada da: Masu rike da masarautun gargajiya, Wakilai daga hukumomin Ilimi, shugabanni daga jami'o'i, da wakilai daga bangaren ilimin firamare, sakandare da kuma makarantun gaba da sakandare da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren ilimin jihar.