Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ummusalama Isiyaka Rabiu daga Jihar Kano a matsayin Kwamishina Mai Kula da Harkokin Gudanarwa (Executive Commissioner, Corporate Services) a Hukumar Kare Hakkin Masu Saye da abokan kasuwanci ta Tarayyar Najeriya (FCCPC).
A bisa tanadin Dokar FCCPC ta 2018, za ta bayyana a gaban Majalisar Dattawa dan tantancewa da amincewa.
Ummusalama, mai shekaru 35, ta kafa Gidauniyar Usir Foundation, da ke taimaka wa marasa galihu da al’umma ta hanyar ilimi, horas dasu don samun ƙwarewa, da ayyukan jin ƙai.
Ta samu digiri a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration), sannan ta shahara a matsayin ƴar siyasa mai kusanci da al’umma, wacce ke fafutukar ganin gwamnati ta haɗa da kowa da kowa, tare da ƙarfafawa matasa da mata wajen shiga harkokin siyasa.