Gwamnatin Tarayya Da Wasu Manyan Kamfanoni Sun Shirya Samar da Jirgin Ƙasa Mai Saurin Gaske a Najeriya akan Kuɗi Dala Biliyan 60

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13082025_160019_passenger-high-speed-train-moves-260nw-1592023696.jpg

Gwamnatin Tarayya tare da kamfanonin De-Sadel Nigeria Ltd. da China Liancai Petroleum Investment Holdings Limited sun shirya fara aikin samar da jirgin ƙasa mai saurin gaske a Najeriya da layin dogo mai tsawon kilomita 4,000 wanda zai ratsa jihohi shida. An bayyana hakan ne a lokacin da kamfanonin suka gabatar da takardar shaida ta kuɗin aikin da darajarsu ta kai dala biliyan 60 ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, a Abuja. A cewar shugaban De-Sadel Nigeria Ltd., Samuel Uko, matakin farko na aikin zai haɗa Legas, Abuja, Kano da Fatakwal, mai tsawon kilomita 1,600, kuma za a kammala shi a matakai daban daban cikin shekaru uku.

Akume ya ce za a binciki takardar shaidar kuɗin don tabbatar da sahihancinta da adadin kuɗin, domin bin ka’idar gwamnati wajen gudanar da irin wannan yarjejeniya. Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki matakai don sauƙaƙa harkokin kasuwanci a ƙasar, tare da tabbatar wa masu saka jari cewa Najeriya a shirye take idan su ma sun shirya. 

Ministan Sufuri, Sa’idu Alkali, ya ce aikin ya dace da manufar ma’aikatarsa ta samar da sufuri mai aminci, araha, da jawo hannun jari daga ƙasashen waje.

A nasa jawabin, Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur (Bangaren Iskar Gas), Ekperikpe Ekpo, ya tabbatar wa masu saka jari cewa Najeriya na da isasshen iskar gas domin aikin, inda ya bayyana cewa ƙasar na da aƙalla tiriliyan 210 na tanadin iskar gas da karin tiriliyan 600 a ƙarƙashin teku. 

Haka kuma, Daraktan Hukumar Kula da Ayyukan Ababen More Rayuwa (ICRC), Dakta Jobson Ewalefoh, ya bayyana cewa gabatar da takardar shaidar kuɗi wajibi ne a irin waɗannan manyan ayyuka, kuma mataki na gaba shi ne tantancewa da tabbatar da yiwuwar aikin.

Follow Us