Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin jari na Naira tiriliyan 1.5 ga Bankin Noma (Bank of Agriculture), wanda ake ganin shi ne mafi girman tallafi da aka taba bai wa harkar noma a tarihin Najeriya.
Wannan sanarwa ta fito ne daga Ma’aikatar Noma a ranar Laraba, inda aka bayyana cewa wannan kudin zai taimaka wajen inganta Bankin Noma a matsayin cibiyar tallafi ga masu noman zamani, musamman matasa da mata masu gudanar da harkokin noma ta hanyar bayar da rance mai sauƙi da horo.
Ministan Noma da Tsaron Abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa aiwatar da Dokar Fasaha da Kirkire-Kirkiren Noma ta Kasa (NATIP) zai sa a samu ci gaba sosai a fannin noma a Najeriya.
Ya ce wannan doka za ta inganta samun kayan aikin zamani, tare da bunkasa noman zamani wanda zai janyo hankalin matasa da mata, ya kuma sa noma ya zama abin more rayuwa, riba, da gasa a tsakanin yan kasa da kasuwa.
Kyari ya kara da cewa NATIP shine ginshikin sauya harkar noma zuwa na zamani mai amfani da fasaha da matasa ke jagoranta, ta hanyar karfafa amfani da injuna na zamani da kuma zurfafa bincike da habbaka kasuwanci.