Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Shirin Samar Da Wutar Lantarki ta Makamashin Hasken Rana har na Naira Biliyan 100

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08082025_202732_FB_IMG_1754664785884.jpg



Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Shirin Gwamnati na Samar da Wutar lantarki ta Hasken Rana ga Muhimman Cibiyoyi ta “National Public Sector Solarization Initiative (NPSSI)” domin samar da wutar lantarki ta hasken rana ga muhimman cibiyoyin gwamnati a fadin kasar nan, tare da fara zuba jarin naira biliyan 100 a matakin farko. Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA) ce za ta aiwatar da shirin, wanda zai bai wa makarantu, asibitoci, ofisoshin gwamnati, wuraren tsaro da sauran muhimman cibiyoyi damar samun wuta mai dorewa. An kaddamar da shirin ne bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin REA, Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, Hukumar InfraCorp da Ma’aikatar Kudi ta MOFI a Abuja.

Shugaban REA, Malam Abba Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa NPSSI wani shiri ne na musamman da gwamnati ta jagoranta domin rage dogaro da man dizal da kuma rage gurɓatar muhalli, tare da bunkasa kirkire-kirkire a masana’antun cikin gida. Ya ce mataki na farko na shirin ya samu cikakken kudin gwamnati, yayin da matakai na gaba za su kasance ta hanyar zuba hannun jarin masu zaman kansu daga cikin gida da kasashen waje, ba tare da dogaro da gwamnati ba. Shugaban Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, Dakta Tanimu Yakubu, ya ce wannan mataki zai taimaka wajen rage gibin samar da wutar lantarki da kuma kara inganta tsarin kashe kudaden gwamnati.

Shugaban Hukumar InfraCorp, Dakta Lazarus Angbazo, ya ce shirin ya zama sabon salo na hada-hadar kudade wajen samar da kayayyakin more rayuwa a Najeriya, domin gwamnati kadai ba za ta iya magance matsalar wutar lantarki ba. Shi ma Darakta-Janar na MOFI, Dakta Armstrong Takang, wanda aka wakilta, ya jaddada muhimmancin kirkirar sabbin tsare-tsaren kasuwanci da za su rage farashin wuta tare da fadada damar samun ta, musamman ta hanyar karkatar da tsarin samar da makamashi daga man fetur zuwa wasu hanyoyi masu dorewa.

Follow Us