Gwamnatin Tarayya Ta Fadakar da Jihohi 32 da Kananan Hukumomi 198 Kan Hatsarin Ambaliyar Ruwa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08082025_130124_gettyimages-2170486225.jpg



Katsina Times 

Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Kasa (NIHSA) ta fitar da sabon gargadin ambaliyar ruwa ga kananan hukumomi 198 a fadin jihohi 32 da Babban Birnin Tarayya Abuja, daga ranar 7 zuwa 21 ga watan Agusta 2025.

A cikin sanarwar da ke dauke da lamba mai nuni 32-25-003-06, Darakta Janar na NIHSA, Mista Umar Ibrahim, ya bayyana cewa wannan gargadi ya biyo bayan karin ruwan sama da kuma tashin matakan ruwa a koguna a sassan kasar nan.

Hukumar ta ce ana sa ran ambaliyar ruwa mai tsanani a kananan hukumomi da al’ummomi sama da 832, tare da yiwuwar katse muhimman hanyoyin sufuri a wannan lokaci.

Jihohin da abin ya shafa sun hada da Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.

NIHSA ta shawarci hukumomin bada agajin gaggawa su hanzarta aiwatar da tsare-tsaren kare rayuka da dukiyoyi, tare da shirin kwashe jama’a daga wuraren da ke cikin hadari.

Hukumar ta kuma bukaci jama’a su ci gaba da bibiyar hasashen mako-mako da take fitarwa na matakin jiha da na kowace al’umma, ta hanyar shafin yanar gizo na www.nihsa.gov.ng, “NIHSA flood dashboard” da kuma shafukan sada zumunta na hukumar.

Wannan gargadi na daga cikin matakan da NIHSA ke dauka na rage illolin ambaliyar ruwa da ake samu duk shekara, wanda ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalata ababen more rayuwa a fadin kasar.

Follow Us