Gwamnatin Katsina Ta Kaddamar da Taron bayyana bukatun Jama’a a Matakin Gundumomi Domin Tsara Kasafin Kuɗi na 2026

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07082025_185543_FB_IMG_1754592775161.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

A wani yunkuri na bunƙasa mulkin dimokuraɗiyya da ƙarawa al’umma tasiri a harkokin gwamnati, Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da tarukan jin ra’ayoyin jama’a a matakin gundumomi domin tsara kasafin kuɗi na shekarar 2026 bisa buƙatun al’umma.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Mai Girma Faruq Lawal Jobe ne ya jagoranci ƙaddamar da shirin a ranar Alhamis, 7 ga Agusta, 2025 a ƙaramar hukumar Kankara, inda aka fara aiwatar da shirin gabaɗaya a mazabu 361 na faɗin jihar.

Faruq Jobe ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na samar da shugabanci nagari daga tushen jama’a, yana mai cewa wannan ba ƙa’ida ce kawai ta tuntubar jama’a ba, manufa da gwamnati ta ɗauka domin zurfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da gaskiya da rikon amana.

“Gwamnatin nan ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Dikko Umaru Radda ta yarda cewar mafi kyawun ra’ayoyin ci gaba su ne waɗanda suka fito daga mutanen da ke rayuwa da matsalolin da muke ƙoƙarin magancewa,” in ji Jobe. “Wannan shiri ne da aka kirkiro musamman domin kusantar da gwamnati da al’umma.”

Ma’aikatar Tsare-Tsare da Tattalin Arziki tare da hadin gwiwar shirin bunkasa al’umma (CDP) ne ke shirya tarukan. Ana sa ran al’umma za su bayyana matsalolinsu, sanya fifiko ga ayyukan ci gaba da kuma bada shawarwari masu amfani da za su shafi unguwanni da kauyuka.

Mataimakin Gwamnan ya ƙara da cewa, wannan mataki na nuna jajircewar jihar wajen bin ka’idojin Ci Gaban da Jama’a ke Jagoranta (CDD) da kuma cika sharudan da ke cikin hadin gwiwar Gwamnati a bude (OGP).

“An umurci dukkan masu riƙe da muƙaman gwamnati da su halarci tarukan a cikin yankunansu. Kuma wajibi ne a gabatar da rahoto daga kowace mazaba zuwa Ma’aikatar Tsare-tsare da CDP domin haɗa bayanan a cikin tsare-tsaren kasafin kuɗi na shekarar 2026,” in ji shi.

Ya ce bayanan da jama’a za su bayar za su taimaka wajen tantance irin ayyukan da suka dace da matakin ƙaramar hukuma, jiha, tarayya ko kuma haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ci gaba na ƙasashen waje.

A nasa jawabin, Kwamishinan Tsare-Tsare da Tattalin Arziki ya bayyana wannan yunkuri a matsayin “sauyi mai ma’ana” daga yadda aka saba, yana mai cewa zamani ya wuce na yin kasafin kuɗi ba tare da sa jama’a ba.

“Wannan ba aikin fasaha kawai ba ne, aiki ne na dimokuraɗiyya. Muna mayar da iko hannun al’umma ta hanyar waɗannan tarukan,” in ji shi. Ya bukaci jama’a da su amfana da wannan dama wajen bayyana bukatunsu da fatansu.

Ya kuma bayyana umarnin Gwamna cewa dole manyan jami’an gwamnati a kowace mazaba su jagoranci taron, kuma dukkan ra’ayoyin jama’a za a rubuta su da muhimmanci a yi la’akari da su a cikin shirin kasafin kuɗi.

Shugaban shirin CDP ya bayyana tarukan a matsayin wata doka da gwamnati ke son kafa domin tabbatar da tsare-tsare da suka dace da al’umma.

“Mun jima muna yin kasafin kuɗi ba tare da sa jama’a ba. Wannan gwamnatin na sauya akalar,” in ji shi. Ya yaba da kokarin Gwamna Radda wajen kafa tsarin da kuma shigar da shi cikin tsarin ayyukan kasafi na gwamnati.

“Wannan tsarin yana nuni da amincewa da ra’ayin al’umma. Muna barin su su faɗi bukatunsu—ko ilimi ne, lafiya, hanyoyi ko ruwa. Muryoyinku za su tsara makomarmu,” in ji shi.

Daga cikin manyan baki da suka halarci ƙaddamarwar akwai Kwamishinan Ilimi na gaba da sakandire, Hon. Isah Mohammed Musa; Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi, Alhaji Sirajo Mikailu; Shugaban Karamar Hukumar Kankara, Hon. Kasimu Dantsoho Katoge; da wasu wakilai daga sarakunan gargajiya ciki har da Alhaji Muhammadu Ahmadu Rambo da Alhaji Aminu Lawal Jobe.

Sauran sun haɗa da Sakataren Jam’iyyar APC na Jiha, Alhaji Umar UT Kankara; Daraktan Hukumar Tara Haraji ta Jiha, Hon. Murtala Muhammad Ayo; wakilan ƙungiyoyin al’umma da sauransu 

Yayin da tarukan ke ci gaba a faɗin jihar, ana sa ran gwamnatin Katsina za ta kafa sabuwar hanya ta shugabanci a buɗe, haɗin kai da gaskiya wajen tsara kasafin kuɗi mai tasiri ga jama’a.

Follow Us