Nasir Salisu Malumfashi
Wani matashi mai fafutukar ganin an samu sauyi a harkar siyasa, Nasir Salisu Malumfashi, ya bukaci tsohon Sanata mai wakiltar yankin Katsina ta Gabas (Shiyyar Daura), Sanata Ahmed Babba Kaita, da ya tsaya takarar kujerar Gwamnan Jihar Katsina a zaben da ke tafe.
Malumfashi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Babba Kaita na daga cikin ‘yan siyasar da suka kafa tarihi wajen nuna kishin kasa da kyakkyawan shugabanci, musamman wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a lokacin da yake a Majalisar Dokokin Ƙasa.
A cewarsa, “Ayyukan Sanata Babba Kaita ba boyayyu ba ne. Jama’a sun gani a fili tun daga lokacin yana a Majalisar Wakilai har zuwa zama Sanata. Ya yi ayyuka ba wai a mazabarsa kadai ba, har da wasu sassan jihar Katsina da ma kasa baki ɗaya.”
Malumfashi ya jaddada cewa Sanata Kaita ya taka rawar gani wajen tallafa wa matasa, yana mai cewa akwai wata dama ta musamman da yake bai wa matasa a duk wata domin ganin sun samu aikin yi ko horo na sana’o’i.
“Sanata Kaita kullum cikin nemawa matasa mafita yake. Kusan kowane wata yana kiran matasa zuwa Abuja domin basu damar aiki ko horar da su. Wannan ne ya sa nake ganin zai fi dacewa ya jagoranci Katsina a matsayin Gwamna,” in ji Nasiru Malumfashi.
Ya kara da cewa babban kalubalen da ke haddasa tabarbarewar tsaro a jihar Katsina shi ne rashin aikin yi, wanda a cewarsa, Babba Kaita ya riga ya fahimci matsalar kuma yana da shirin magance ta tun kafin yanzu.
“Mun tabbatar cewa rashin aikin yi ne ke haddasa rashin tsaro a yankunanmu. Kuma Sanata Babba Kaita na daya daga cikin ‘yan siyasa da ke da hangen nesa da kishin talaka,” in ji shi.
Nasiru Malumfashi ya bayyana cewar ko da Sanata Kaita zai tsaya takara a kowace jam’iyya, yana da yakinin cewa al’umma za su zabi mutum bisa cancanta da nagarta, ba wai jam’iyya kadai ba.
“Kowa da ya san Sanata Babba Kaita ya san mutum ne mai gaskiya da rikon amana. Kuma al’umma suna kallon nagarta ne ba wai jam’iyyar siyasa ba,” ya jaddada.
Daga ƙarshe, ya bukaci al’ummar Katsina su goyi bayan duk wani dan takara mai kishin kasa irin Sanata Babba Kaita mai muradin ceto jihar daga matsalolin da ta fada ciki, yana mai cewa Babba Kaita na da dukkan kyan halayen da ake bukata wajen jagorantar jihar zuwa tudun mun tsira.