Fitaccen Dan Wasan Damben Duniya Hogan Ya Rasu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24072025_164913_FB_IMG_1753375682193.jpg


Fitaccen gwarzon damben duniya kuma zakaran WWE, Hulk Hogan, wanda a asalin sunan sa na gaskiya Terry Gene Bollea, ya rasu ranar Alhamis yana da shekaru 71, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta Clearwater da ke Florida, tare da hukumar WWE suka tabbatar.

“WWE na cikin jimami da bakin ciki da samun labarin rasuwar gwarzon na WWE Hall of Fame, Hulk Hogan,” in ji sanarwar da kamfanin ya fitar. “Hogan na daga cikin fitattun mutane a harkar nishadin duniya. Ya taka gagarumar rawa wajen bunƙasa WWE a duniya, musamman a shekarun 1980. 

Hogan ya fara harkar sana'ar dambe a shekarar 1977, inda ya yi fice a manyan hukumomi kamar World Wrestling Federation (WWF – yanzu WWE), World Championship Wrestling (WCW), da kuma Impact Wrestling. Amma wasanninsa a WWE a cikin shekarun 1980 ne suka ɗaga darajarsa da kamfanin zuwa matakin duniya.

Daya daga cikin kalmominsa da suka fi shahara shi ne: “Whatcha Gonna Do When Hulkamania Runs Wild On You!” – wanda ke ƙarfafa magoya bayansa yayin da yake jan kunnensa domin jin yadda suke ihun goyon baya. Ya fito a wasannin WrestleMania har sau goma, inda ya jagoranci manyan gasar sau takwas. A WrestleMania ta farko a 1985, ya yi tag da Mr. T suka doke Paul Orndorff da Roddy Piper.

A shekarar 1985, yayin wata hira a talabijin tare da jarumi Richard Belzer, Hogan ya sa Belzer cikin rikici har sai da ya suma, wanda hakan ya kai ga shari’a da sulhu a 1990.

Hogan ya bar WWE a tsakiyar shekarun 1990 zuwa WCW, inda ya fuskanci kalubalen rashin farin jini daga masoya. A 1996 ya ƙirƙiri sabon hali na "Hollywood Hogan", wanda ya zama shugaban ƙungiyar "New World Order" a WCW.

Ya dawo WWE a 2002, inda ya fafata da Dwayne “The Rock” Johnson a WrestleMania X8, kuma magoya bayansa suka sake rungumarsa da murna.

A 1994, an tuhumi shugaban WWE Vince McMahon da bada kwayoyin ƙara ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba, Hogan ya shaida a kotu cewa ya taɓa amfani da su amma ba daga umarnin McMahon ba. Haka kuma a 2015, wani rikodin da ya nuna Hogan yana furta kalaman wariyar launi ya bayyana, wanda hakan ya kai ga korarsa daga WWE da cire sunansa daga Hall of Fame na wucin gadi.

Sai dai daga bisani ya nemi gafara, yana mai cewa: "Ba ni da wariyar launi, kuma abin da na faɗa ba daidai ba ne, kuma na yi nadama."

An sake karɓar Hogan a WWE a 2018, inda ya jagoranci WrestleMania 37 tare da WWE Superstar Titus O’Neil a 2021. A watan Yuli 2023 ya sanar da ɗaura auren sa da malamar yoga Sky Daily, kuma suka yi aure a Satumba 2023.

A watan Yuli 2024 ya hau dandalin taron Republican National Convention, inda ya nuna goyon baya ga tsohon shugaban ƙasa Donald Trump, wanda ya kira da “shugaban ƙasa mafi kishin ƙasa da na sani a tsawon shekaru 35.”

Hogan ya yi aure sau uku: Na farko da Linda Bollea daga 1993 zuwa 2009, inda suka haifi yara biyu – Brooke da Nick. Daga bisani ya auri Jennifer McDaniel a 2010 amma suka rabu a 2011. Sai kuma Sky Daily, matar da ya aura a 2023, wacce ta rage masa a duniya tare da yaransa biyu.

Hogan ya bar duniyar nan yana daga cikin fitattun taurarin damben duniya, wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da rawar da ya taka ba.

Follow Us