Tsaro Ya Inganta A Jihar Zamfara, Inji Gwamna Lawal Yayin Tattakin Zaman Lafiya Na Tarihi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30052025_182627_IMG-20250530-WA0144.jpg


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce tsaro ya inganta sosai a jihar.

Gwamnati ta shirya wani tattaki ne a ranar Alhamis mai taken ‘Tattaki Don Zaman Lafiya’ don bikin cikar gwamnatin Gwamna Lawal shekaru kan karagar mulki.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, an shirya wannan tattaki ne domin ƙarfafa zaman lafiya da ƙarfafa gwiwar jama’a su haɗa kai don yaƙar duk wani nau’i na miyagun laifuka.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an fara tattakin zaman lafiyar ne daga gidan gwamnati inda aka zarce zuwa dandalin Freedom da ke tsakiyar Gusau, babban birnin jihar.

Da yake jawabi ga ɗimbin mutanen da suka halarci wannan tattaki, Gwamna Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kawar da duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar, tare da mai da hankali sosai kan ‘yan bindiga.

Ya ce, “A yau mun fito dubunnan mu domin mu yi tattakin samun zaman lafiya, domin mu sanar da duniya cewa Zamfara ta samu ci gaba sosai ta fuskar tsaro.

“Gwamnatina ta ba da himma da kayan aiki masu yawa don ƙarfafa sojoji, tattara bayanan sirri, da haɗa kai don dawo da zaman lafiya a jihar.

"Mun sami gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da 'yan bindiga, yawancin wuraren da ake fama da rikici a baya, a halin yanzu sun kasance cikin kwanciyar hankali. Hanyoyin da a da ba a iya wucewa, a yanzu matafiya na wucewa lami lafiya cikin 'yanci.

"Kuna iya ganin yadda mutane ke tafiya cikin walwala tare da gudanar da ayyukansu na yau da kullum da kuma yadda suke taruwa cikin farin ciki don yin tattakin samar da zaman lafiya. Wannan ya nuna a fili cewa mutanenmu sun samu zaman lafiya kuma suna son zaman lafiya. Hakan kuma ya nuna cewa jama'a sun fahimta kuma sun yaba da abin da gwamnatin jihar ke yi don inganta zaman lafiya."

Follow Us