Daga Wakilanmu, Jihar Katsina
Binciken da wakilanmu suka gudanar ya bankado wata babbar matsala da ta dade tana faruwa a hukumomin ilimin kananan hukumomi (LEAs) a fadin Jihar Katsina — matsalar da ta zarce abin da aka fara bayyana a karamar hukumar Bakori.
Abin da ya fara a matsayin rahoton cire albashi da cin zarafin malamai a LEA ta Bakori, ya zamo hanya ta bayyana cin hanci da almundahana da suka wuce misali. Binciken ya tabbatar da cewa wannan lamari bai tsaya a Bakori kadai ba, kusan dukkan LEAs a jihar na fama da irin wannan matsala — har da wasu kananan hukumomin gaba ɗaya.
Rashin Biyan Albashi:
Malaman makaranta daga kananan hukumomi daban-daban kamar su Bakori, Funtua, Kankia, Malumfashi, Jibiya da Daura sun tabbatar da cewa ana hanasu albashi ba tare da wani karin bayani ba. Wasu na shafe watanni ba tare da samun hakkinsu ba, kuma idan an dawo da biyan, ba a maido musu da albashin da aka hana su a baya.
Wani malami daga Jibiya da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Abin yana kamar caca ne — ba ka san ranar da za a hana ka albashi ba, ko ko da za ka samu cikakke.”
Ma’aikata Na Bogi:
Binciken ya gano yadda wasu mata malamai da suka bar jihar domin haduwa da mazajensu a wasu yankuna na kasar nan, ke ci gaba da karɓar albashi, duk da ba sa koyarwa. Wadannan malamai na daukar marasa aikin yi su dinga koyarwa a madadinsu, suna biyansu kadan daga cikin albashin — duk da sanin wasu jami’an LEA.
Haka kuma, akwai wasu da suka bar aiki suka koma gwamnatin tarayya ko kamfanoni masu zaman kansu, amma har yanzu sunansu na cikin jerin masu albashi a LEA. Wadannan su ne ake kira “ma’aikatan bogi”, wadanda ke bayyana ne kawai lokacin tantance ma’aikata.
Sayen Karin Girma: Cancanta Ta Zama Kudi
Wani bangare mai tada hankali da binciken ya tona shi ne sayar da karin girma. Malamai daga hukumomi daban-daban sun bayyana cewa ana bukatar su biya kudi kafin su samu karin girma da ya dace da su.
“Idan sakon karin girma ya fito, sai ka biya kafin ka samu,” in ji wani malami daga LEA Bakori. “Wanda bai da kudi, zai cigaba da zama a matsayinsa na shekaru da dama.”
Rashin Adalci da Son Kai:
An kuma gano yadda ake fifita ’yan uwa da abokai wajen nada shugabannin makarantu. A wasu lokuta, ana nada malamai masu Grade Level 9 ko 10 shugabanni a kan wadanda ke da manyan mukamai irin su Grade Level 13 ko 14.
Wani babban malami daga Bakori ya bayyana cewa: “Wannan tsarin yana karya kwarin gwiwa. Komai dangantaka ne, ba cancanta ba.”
Zaɓen malamai da ake turawa horo da tarurruka (workshops) ma na tafiya ne bisa son zuciya. Wadanda ke da kusanci da shugabanni su ke amfana, yayin da wadanda suka fi cancanta ke ci gaba da zama a gefe. Har ila yau, abincin da ake bai wa mahalarta taruka ba ya kai matsayin da ya dace, duk da makudan kudin da ake warewa a kasafi.
Kira Ga Gwamnati: A Fadada Bincike
Yanzu da abin da ke faruwa ya bayyana fili, masana harkar ilimi da ’yan kasa na kira ga Gwamna Malam Dikko Umaru Radda da ya fadada bincike zuwa dukkan kananan hukumomin jihar.
“Gwamna ya kamata ya fadada bincike fiye da Bakori. Tsarin LEA gaba ɗaya ya samu tangarda,” in ji wani tsohon jami’in ilimi. “Ba wani karamar hukuma kadai ke fama da wannan matsala ba.”
Malaman makaranta a fadin Jihar Katsina na ci gaba da fuskantar halin kunci da zalunci. Ana hana su hakkinsu, ana tauye su, kuma ana rage musu daraja. A daidai lokacin da tattalin arzikin kasa ke fama da kalubale da karancin aikin yi, buƙatar gyara da adalci a tsarin ilimi ba ta taɓa zama dole kamar yanzu ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Katsina da Hukumar SUBEB na ci gaba da gudana, yayin da al’umma ke ƙara matsa lamba domin samun gaskiya da sauyi mai ma’ana.