Mataimakin Gwamnan Katsina ya jagoranci kwamiti don Halartar Taron Ma'adinai na Afirka a Nairobi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09052025_200751_FB_IMG_1746821232987.jpg



Wata tawaga daga Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna, Malam Faruq Lawal Jobe, ta halarci babban taron ma’adinai na Afirka da aka gudanar daga 7 zuwa 8 ga Mayu, 2025, a Radisson Blu Hotel da ke birnin Nairobi, Kenya.

Taken taron shi ne “Amfani da Ma’adinai Don Cigaban Tattalin Arziki: Binciken Hanyoyin Samun Kuɗaɗen Zuba Jari,” inda manyan masu tsara manufofi da kwararrun masana harkar kuɗi daga sassa daban-daban na nahiyar suka halarta.

Tawagar daga Katsina ta haɗa da manyan jami'an gwamnati, inda suka shiga tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan ci gaban harkar ma’adinai. Mataimakin Gwamna Jobe ya bayyana taron a matsayin mai fa’ida, tare da yabawa Gwamna Dikko Umaru Radda bisa amincewa da halartar taron.

Taron ya ƙare da miƙa takardun shaida ga mahalarta, alamar jajircewar Katsina wajen amfani da albarkatun ma’adinanta domin ci gaban tattalin arzikin al’umma.

Follow Us