Matakin Gwamnatin Nijar Na Maye Gurbin Harshen Faransa Da Hausa: Mahimmanci Ga Ci Gaban Ƙasa Da Tasiri A Yammacin Afirka

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16042025_182858_IMG-20250416-WA0065.jpg


Daga: Adamu S Ladan 

A ‘yan kwanakin nan, hukumomin kasar Nijar sun dauki mataki mai tarihi na dakatar da amfani da harshen Faransa a matsayin harshen gwamnati, tare da maye gurbinsa da harshen Hausa – daya daga cikin manyan harsunan ‘yan asalin kasar.

 Wannan mataki ba kawai sauyi ne na harshen sadarwa ba, har ila yau wata alama ce ta fafutukar dawo da martabar al’ada, tarihi da yancin kai na al’umma.

Mahimmancin Wannan Mataki Ga Ci Gaban Nijar ba ya misaltuwa musamman wajen Karfafa Al’adu da Asalin Ƙasa. Harshen Hausa na da dogon tarihi da alaka da rayuwar yau da kullum ta Hausawan Nijar. Mayar da shi harshen gwamnati na nufin dawo da al’ummar ƙasar da asalin su, tare da tabbatar da cewa al’adun su da harshensu sun samu girmamawa a matakin kasa. Wannan zai kara jin dadin jama’a da sha’awar shiga harkokin mulki da ci gaba. Don an kauda wariya da amfani da bakon harshen turanci ya jefa da dama mutanen kasar da ba sa iya amfani da shi duk kuwa da dimbin basira da hikima da Allah Ya ba su. 

Saboda haka,  amfanin harshen gida watau, Hausa zai kara saukaka huldar gwamnati da jama'a.Yawancin ‘yan Nijar ba su da cikakkiyar fahimta ko iya magana da harshen Faransa, wanda ke zama cikas ga samun saukin fahimtar manufofin gwamnati. Aikin gwamnati da hulɗar jama’a da harshen da suke fahimta zai kara tasiri, yarda da kuma ingancin aiwatar da tsare-tsare.

Wannan mataki kuma ya kara jaddada gwagwarmayar Kawar da dabarar mulkin mallaka da 'yan mulaka'u ke amfani da ita wajen tabbatar da dakushe cigaban Afuruka. Amfani da harshen Faransa tsawon shekaru kamar yadda turancin Ingilishi ya ke a Najeriya ya kasance wani nau’i na ci gaba da tasirin mulkin mallaka. Wannan sauyi lalle wata hanya ce ta nuna cikakken ‘yancin kai da kokarin gina kasa bisa ginshikin ƙasaitar al’ummar ta.

Wannan mataki zai karfafa matsayin harshen Hausa ba kawai a Nijar ba, har da Najeriya, Ghana, da Kamaru, da Chadi da sauran kasashe da Hausawa ke rayuwa. Yana da yiyuwar hakan zai sa kasashen makwabta su fara duba yiwuwar amfani da harshen Hausa a wasu fannoni na gwamnati ko hulda da jama’a.

Haka ma matakin zai iya kawo hadin Gwiwa tsakanin Hausawan yanki Afuruka ta yamma. Yayin da harshen Hausa ke kara samun karbuwa a matakin gwamnati a Nijar, hakan zai karfafa zumunci, hulda da fahimtar juna tsakanin Hausawan kasashen da ke makwabta. Wannan na da tasiri sosai wajen inganta harkokin kasuwanci, ilimi, da hadin kan al’umma.

Wannan mataki wata dama ce ta bunkasa Ilimi da harshen. Harshen Hausa da ke da dimbin adabi, tarihi da hikima zai kara samun karbuwa a matsayin harshe na ilimi. Makarantu, kafafen yada labarai, da cibiyoyin kimiyya za su fara duba mahimmancin Hausa wajen yada ilimi da bayanai. Musamman a Arewacin Najeriya da rashin amfani da harshen gida a jawo koma baya gaya a harkar ilmi. 

To, wane mataki ya kamata hausawan sauran kasashen afrika ta yamma za su dauka don cimma burin maida harshen Hausa a matsayin harshen hulda a gwamnatance musamman yankin arewacin Najeriya da Ghana da Kamaru da Chadi  da ke amfani da harshen wajen huldodin yau da kulum?

Wannan tambaya na da matukar muhimmanci, domin tana tabo wata babbar dama da Hausawa da masu jin Hausa ke da ita wajen karfafa matsayin harshensu a matsayin harshe na hulda a matakin gwamnati a yankin Yammacin Afirka. Ga wasu matakai da za a iya dauka don cimma wannan buri, musamman a Arewacin Najeriya, da Ghana da Kamaru.

1. Inganta Hausa a Ilimi da Makarantu
• Rike wa da koyar da Hausa a makarantu, musamman tun daga matakin farko (primary) har zuwa gaba da sakandire. Idan yara sun tashi da Hausa a matsayin harshe na koyarwa, hakan zai sa su girma da jin dadin amfani da shi a rayuwar yau da kullum. Sabanin halin da ake ciki yanzu inda yaran su batan- baka-tantan ba su iya turancin ba sun kuma saki Hausa.
• Kafa cibiyoyin bincike da koyar da Hausa a jami’o’i na gida da kasashen waje domin zurfafa ilimi da adabin Hausa.
• A Najeriya, ana bukatar karfafa amfani da Hausa a fannin ilimi da kwasa-kwasai na musamman a jami'o'in Arewacin Najeriya.
2. Tallafa wa Kafafen Yada Labarai da Littattafan Hausa
• Gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu su rika daukar nauyin shirye-shiryen Hausa a kafafen yada labarai na kasa da kasa kamar NTA, Radio Nigeria, GTV (Ghana), CRTV (Kamaru) da sauransu.
• Wallafa littattafai da mujallu da jaridu a Hausa, wanda zai kara bunƙasa karatu da fahimtar harshen a cikin al’umma.
• A samar da manhajojin wayar salula da na kwamfuta da ke amfani da Hausa domin amfani a makarantu da ma’aikatun gwamnati.
3. Kafa Kungiyoyi da Harsashen Hausa A Matsayin Agenda
• Hausawa a kasashe daban-daban su kafa kungiyoyin kare da bunkasa Hausa, masu hada kai da gwamnati da jama'a, domin su rika matsa lamba da gabatar da bukatu ga gwamnati.
• Kungiyoyin irin su Hausa Language Promotion Council ko Hausa Cultural Renaissance Forum na iya zama cibiyoyi na hadin kai da tsara dabaru.
4. Shiga Siyasa da Tuntuba da Shugabanni
• Hausawa a bangarori daban-daban su rika tuntubar ‘yan siyasa da masu rike da madafun iko domin su fahimci bukatar amfani da Hausa a matsayin harshe na hulda a hukumomi, musamman a yankunan da Hausawa ke rinjaye.
• ‘Yan majalisa, ‘yan kwamitin ilimi da yada labarai a kasashe irin su Najeriya, da Ghana, da Kamaru za su iya bayar da gudunmawa wajen kawo sauyi a dokokin gwamnati.
5. Haɗin Gwiwar Yankin Yammacin Afirka
• A gina hadin gwiwa tsakanin kasashen da Hausa ke yawo kamar Najeriya, Nijar, Ghana, da Kamaru, da Chadi domin samar da tsarin hadaka kan harshen Hausa – kamar su shirya tarukan harshe, ilimi da al’adu.
• Wannan na iya taimaka wajen karɓar Hausa a matsayin harshe na yanki kamar yadda ECOWAS ke da yunkurin yare iri-iri.
Kammalawa:
Matakin da Nijar ta dauka wata kafa ce ta kirkire-kirkire da martaba al’umma. Yana wakiltar sabuwar hanya ta gina kasa bisa harshe, al’ada da tsari na cikin gida. Harshe yana da matukar muhimmanci wajen gina tunani, kawo hadin kai da tabbatar da yanci. Nijar ta bude sabuwar kofa ga sauran kasashen Afirka don tunani mai zurfi kan rawar da harsunan gida za su taka wajen ciyar da kasashen gaba. Wannan mataki na da karfi sosai wajen karfafa al’ummar Hausa da ba su wani sabon mataki na fahimta da girmamawa a matakin yanki da duniya baki daya.

Harshen Hausa na da dimbin tarihi, yawan masu amfani, da kuma ƙwarewa a bangaren sadarwa. Wannan shi ya sa kasashen da ke da'awar cigaba su rungumi harshen wajen amfani da shi a kafafen yada labarai don cimma burin su na siyasa da tattalin arziki.  Abin da ya rage ma Hausawa shi ne tura karfi da haɗin kai daga gwamnati, jama’a, da masu ruwa da tsaki, domin karfafa matsayin Hausa ba kawai a huldar yau da kullum ba, har a doka da tsarin mulki. Tsarin mulki a Najeriya musamman ya bada dama da ayi amfani da harshen gida a majalisun tarayya, hadda ma koyar wa a matakin farko na makarantu. 
Yanzu da Nijar ta fara jagoranci, lokaci ya yi da sauran kasashen da Hausawa ke da rinjaye su bi sahu, domin a gina yare a matsayin tushen ci gaban al’umma da yancin kai.

Adamu S Ladan.

Follow Us