Katsina Charity Support Foundation sun 'yantar da mutane 31 da ciyar da mutane 3000, da taimakon magidanta 2000

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30032025_095432_IMG-20250330-WA0012.jpg

PRESS RELEASE 

A wannan shekarar albarkar watan Ramadan KATSINA CHARITY SUPPORT FOUNDATION ta yi nasarar 'yantar da mutane 31 daga gidan  yari maza 11 mata 20.

Ta kuma yi nasarar ciyar da mutane dubu uku da ke asibiti da gidan baƙi na katsina.
 
Ta kuma yi nasarar ba magidanta 2,000 abinci da kuɗin cefane.

Wannan yana ƙunshe ne cikin rahotonsu na Azumin wannan shekarar wanda kwamitin da ke kula da wannan aikin mai mutane 19 ya tabbatar da shi sannan shugaban kwamitin Alhaji Lawal Aliyu Daura MNI, tsohon shugaban ma'aikata na jihar Katsina da Muƙaddashin Sakataren Foundation ɗin Muhammad Ɗanjuma Katsina suka sanya wa hannu.

An kafa wannan Foundation a shekarar 2020 domin tallafa wa marasa galihu a lokacin watan Ramadan mai alfarma.

Foundation ɗin yana da membobin gudanarwa mutane 21, waɗanda suka fito daga duk faɗin jihar Katsina. Daga cikinsu akwai Alhaji Lawal Aliyu Daura Mni, Alhaji Lawal Rufa'i Safana, Alhaji Dauda Kurfi, Alhaji Lawal Attahiru Bakori, Alhaji Ibrahim Ahmed Katsina, Alhaji Sabo Musa Hassan, Alhaji Muntari Lawal Ƙofar Soro, Barista Ahmad Ɗanbaba Batsari. Dakta Habib Umar FMC. Hajiya Mariya Abdullahi Bakori, Hajiya Murja Yusufu Saulawa, Hajiya Halima Audi, Hamza Yusufu Jibia, Kabir Umar Saulawa Al-Amin Isah, Alhaji Yakubu Suleiman da Yusufu Ibrahim, Alhaji Tukur Hassan Ɗan Ali.
Foundation ɗin na tara kuɗin shi, daga   gudummuwar da membobin Katsina Times Forum da ke dandalin Whatsapp kan tara, daga dubu ɗaya har zuwa miliyan ɗaya.

A wannan shekarar sun tara Naira miliyan shida da dubu dari ɗaya da suka yi wannan aikin da su.

Yana da kwamitocin guda uku na farko masu kula da sako mutane daga gidan yari don su yi Azumi a gida. 

Na biyu masu kula da dafa abinci suna kai wa asibitici da gidan baƙi. 

Na uku masu sayen ɗanyen abinci suna kai wa unguwanni marasa galihu da ke gefen birnin Katsina suna ba magidanta gida, ɗanyen abinci da kuɗin cefane.

Daga shekarar 2020 da suka fara aikin su zuwa 2025, sun tara da raba miliyan 30 ga mabuƙata a cikin Ramadan. 

Aikin Foundation ɗin an gina shi ne bisa cikakkiyar goyon baya da aiki kafaɗa da kafaɗa da  kamfanin jaridun Katsina Times Media Group, masu buga jaridun Katsina Times, Online Katsina City News, da jaridar Taskar Labarai.

Yana kuma samun cikakkiyar goyon bayan Mobile Media Crew, Katsina Post, Verified News da Jakadiya Redio and TV.

Follow Us