Gwamnati Nijeriya Ta Ci Gaba da Murkushe ‘Yan Bindiga

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28032025_120914_Screenshot_20250328-130619.jpg

Gwamnati Ta Ci Gaba da Murkushe ‘Yan Bindiga

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a yaƙi da ‘yan bindiga tun bayan hawanta mulki, inda jami’an tsaro suka kawar da wasu fitattun shugabannin ‘yan ta’adda da mabiyansu da dama.

Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman Kan Harkokin Jarida (Print Media), Abdul'aziz Abdul'aziz, ya bayyana cewa an murƙushe wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga da suka addabi al’umma, wanda hakan ya taimaka wajen rage matsalar tsaro a yankunan da abin ya shafa. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai:

1. Ali Kachalla/Ƙawaje
2. Kachallah Dogo Kwaddi
3. Lawali Dodo
4. Ɓoderi
5. Sani Wala-birki
6. Kachallah Hana-Zuwa
7. Damina
8. Kachalla Sani Dangote
9. Kachalla Adamu
10. Halilu Sububu
11. Baleri
12. Modi Modi
13. Kachalla Mai Shayi
14. Kachalla Tsoho Lulu
15. Ibrahim Nagure
16. Kachalla Makore
17. Bulak
18. Tukur Sharme
19. Hassan Ɗantawaye
20. Ɗan-Isuhu

Abdul’aziz ya ƙara da cewa, ko da yake matsalar ‘yan bindiga ba ta ƙare gaba ɗaya ba, kashe waɗannan manyan shugabanni ya taimaka matuƙa wajen dawo da zaman lafiya a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi sassauci ba a yaƙi da ta’addanci, tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a duk faɗin ƙasar.

Follow Us