Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times
Shugaban Hukumar Tsaro ta Civil Defiance (NSCDC) reshen Jihar Katsina, Comdt. Aminu Datti Ahmad, ya raba kayan abinci ga masu bukata ta musamman ta hannun mataimakiyar shugaban majalisar matasa ta jihar, Amb. Khadija Suleman Saulawa.
An gudanar da rabon ne a ranar Laraba, 26 ga Maris, 2025, a wani yunkuri na tallafa wa al’umma, musamman a lokacin azumin watan Ramadan.
Da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Comdt. Datti ya bayyana cewa tun farkon Ramadan yake gudanar da rabon kayan abinci ga mabukata, domin rage musu radadin halin da ake ciki. Ya ce bisa ga wannan manufa ne ya ga dacewar fadada shirin zuwa ga masu bukata ta musamman, tare da hadin gwiwar Amb. Khadija Suleman Saulawa, domin tabbatar da cewa an kai tallafin ga wadanda suka fi bukata.
Kayan tallafin sun hada da shinkafa, taliya, makaroni, sukari, da sauran kayayyakin abinci, inda aka rarraba su ga mutane 38, ciki har da mata, maza, samari da 'yan mata masu bukata ta musamman.
Wadanda suka amfana da tallafin sun nuna matukar godiya ga NSCDC da kuma Amb. Khadija Suleman Saulawa, bisa wannan karamci, tare da yin addu’ar fatan alheri ga duk masu daukar nauyin tallafin.