AN KUSA TSERATAR DA JANAR TSIGA, AMMA......

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23032025_090128_FB_IMG_1742720386968.jpg

Daga Muazu Hassan 
@Katsina Times 

Wani binciken musamman da jaridun KATSINA TIMES ya tabbatar da gamayyar jami'an tsaron Nijeriya sun kai hari har maɓoyar da ɓarayin daji suke ajiye tsohon Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi Wa Ƙasa Hidima ta Nijeriya (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya, ba a samu nasarar ceto shi ba.

Ɓarayin daji sun yi garkuwa da Janar Tsige ne a ranar 5 ga Fabrairun, 2025 a ƙaramar hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.

Tuni dai ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) da kuma ta Dattijan Jihar Katsina (KEF), sun buƙaci gwamnatin da kuma rundunar sojojin ƙasar, su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun ceto Janar Tsiga daga hannun 'yan bindiga.

Wata majiya mai tushe ta shaida KATSINA TIMES cewa, farmakin da aka kai tsararre ne, da nufin tarwatsa ɓarayin dajin ya sa su nemi mafaka su kuma waɗanda ake garkuwa da su su gudu zuwa kusa da inda sojan ƙasa suke da za su iya ba su kariya da ɗaukar su zuwa ga tudun-mun-tsira.

Bincikenmu ya tabbatar da tsarin harin ya yi nasara, hatta inda aka kai shi an dace, an kashe ɓarayin daji da yawa, wanda wannan ya ba da damar duk waɗanda ake tsare da su a dajin suka bar inda suke, suka kama gudu zuwa wata mafaka ta daban.

Kamar yadda aka tsara, duk suka fada hannun jami'an tsaron da suka yi kwanton-ɓauna a wurare daban-daban.

Majiyarmu daga cikin jami'an tsaron sun faɗa mana cewa daga cikin waɗanda suka faɗo hannun jami'an tsaron har da waɗanda aka yi garkuwa da Janar Tsiga tare da su.

Ɗaya daga cikin waɗanda ake tsare da su a dajin tare da Janar Tsiga ya faɗa wa jami'an tsaron da suka ceto su cewa, suna tare da Janar Tsiga a waje ɗaya. Sai ga wani jirgi marar matuƙi na shawagi. "Daga nan sai ga wasu jiragen yaƙi, nan ɓarayin suka tarwatse suka barmu. Ko da muka ga haka sai muka fara gudu," in ji shi.

Ya ce shi yana tare da Janar Tsiga har sun fara tafiya tare, sai ya ce shi ba zai iya  ba.

Ya ce, "Na yi, na yi da Tsiga, har na ce masa kalli jirage a sama na shawagi har mu kai inda za mu samu taimako ɓarayin nan ba za su dawo ba, amma Janar Tsiga saboda girman shekaru da wahalar zaman daji ya ce shi ba zai iya tafiya ko gudu ba."

Ya ce, "Da na ga ya kasa, sai kawai ni na bi daji, kuma ina cikin tafiya na faɗa hannun sojoji. Yadda na tsira ke nan. A can na baro Tsiga."

Jaridun KATSINA TIMES sun tabbatar da wannan da ya gudo daga inda ake tsare da Janar Tsiga, ya koma garin Tsiga cikin 'yan'uwa da dangi, kuma ya tabbatar da abin da muka samu labari.

Majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa tun bayan yin garkuwa da Tsiga gwamnatin Katsina da haɗin gwiwar jami'an tsaron tarayya suke bin lamarin yadda za su tabbatar ya samu 'yanci.

A daren da aka sace Janar Tsiga 'yan CWG na garin na tsiga suna sa ido da suka sami tabbacin kamar ba komai suka koma Bakori. 

Bayan tafiyarsu aka kai wa garin hari,aka tafi da tsiga, wanda ya nuna akwai aikin infoma.

Dabar ɓarayi uku ce ta shirya ta'addancin, sune dabar Guddal, Ɗanduna da Babaro.

Ɓarayin sun fara ajiye shi a wajen dajin da ke wajen Ƙanƙara da Faskari.

"Muna bin lamarin daki-daki, muna tattara bayanai har mun fara tsara kai hari sai muka ji cewa sun ɗauke shi daga nan sun mayar da shi wajen Ɗanmusa," in ji wani jami'in tsaron da yake da masaniya a kan ƙoƙarin ƙwato Janar Tsiga.

Labarai sun tabbatar mana wajen Dutsen Ɗinya, daidai wajen dazuzzuka da duwatsun da ke Ɗanmusa, inda barayin nan su Buzare da Larbi da Manore suke da ƙarfi.

"Bayanan sirri da na tauraron ɗan'adam sun tabbatar mana da ganin gungun ɓarayi da muggan makamai a wajen, da alama suna gadin wasu tsararru ne. 
Nan da nan muka tsara kai harin da ba za mu cutar da waɗanda ake tsare da su ba. 
Mun kashe su da yawa, kuma wasu tsararrun sun gudu, amma muka gano Janar Tsiga ba ya wajen," in ji wani soja da ke cikin gamayyar jami'an tsaron da suka yi aikin wanda bai yarda a bayyana sunansa ba.

Wani da ke cikin gamayyar jami'an tsaron ya faɗa mana cewa, 
"Mun samu jin wata murya a wayar tarho ta wani 'bandits' na faɗa wa wasu 'yan'uwansa cewa, Janar Tsiga yana wajensu a dutsen Dargaza a yankin Maidabino da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa. 

"Wannan murya ita sanya aka fara bincike daga baya aka samu tabbacin haka. Sai kuma aka fara tsara ya za a kai hari wajen don kuɓuto da kowa har da Janar Tsiga.

"Hotunan tauraron ɗan'adam da hotunan jirage marasa matuƙi da na jiragen sama suka tabbatar mana da tsarin yadda wurin yake," in ji wani jami'in farin kaya da yake cikin shirin.

A ranar da aka tsara kai harin ba wanda ya sani sai waɗanda abin ya shafa. Don an tabbatar da Janar Tsiga yana wajen.

Jirage shida masu saukar ungulu da marasa matuƙi suka tashi. Sai sojan ƙasa da suka yi tunga a wasu maɓoya daban-daban don ɗaukar matakin da ya dace.

"Bandits da yawa sun baƙunci lahira, kuma an ceto mutane da yawa. Jiragen 'drones' sun riƙa yawo ko za su hango Tsiga don kai masa ɗauki a taho da shi, amma ba su gan shi ba," in ji ɗaya daga cikin jami'an da suka yi aikin.

Shi ma wani da aka ceto ya faɗa mana cewa Janar Tsiga ya fara tafiya sai ya kasa, don haka sai ya samu wani dutse ƙasan wani itace ya zauna ya ce ba zai doguwar tafiya ba," in ji wani yaron da ya tsero daga inda suke tsare tare da Tsiga.
Ko lokacin da barayin dajin suka je tafiya da Tsiga ana fara tafiya, ya fada masu bai iya doguwar tafiya,sai dai sato wani Babur sukayi, suka Dora shi sama zuwa inda suka boye baburansu.
Iyalan tsiga sun tabbatar yana fama da ciwon suga da hawan jini kuma bai tafi da magungunan da yake sha ba.kila shi yasa jikin sa ya saki.

Bayan jiragen sun tarwatsa ɓarayin, suna ta shawagi ƙasa-ƙasa, da ba su ga Tsiga ba suka tafi.

Zargin da ake jiragen na tafiya ɓarayin suka dawo suka sake kama Tsiga a inda yake zaune.

Binciken KATSINA TIMES ya tabbatar sau huɗu gamayyar jami'an tsaro na kai manyan farmaki daban-daban don yunƙurin ƙwato Janar Tsiga ban da waɗanda suka yi nasara, amma yanayin jikin Tsiga bai ba shi damar ya iya isa inda za a gan shi a ceto shi ba.
@ Katsina times 
Www.katsinatimes.com 
@ jaridar Taskar labarai 
@ www.taskarlabarai.com 
Duk a shafukan sada zumunta.07043777779.08057777762.email.
newsthelinks@gmail.com

Follow Us