Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa wani kwamitin nazarin takardar shawarwari (White Paper Committee) don duba rahoton da kwamitin binciken makarantun kiwon lafiya ya gabatar. Rahoton ya mayar da hankali kan Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jihar Katsina da sauran makarantun koyar da lafiya masu zaman kansu a fadin jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar (SGS), Abdullahi Garba Faskari, ne ya kaddamar da kwamitin a madadin Gwamna Malam Dikko Umar Radda a ranar Talata, 18 ga Maris, 2025. Matakin kafa kwamitin ya biyo bayan taron majalisar zartaswa na biyar da aka gudanar ranar Laraba, 12 ga Maris, 2025.
Ayyukan da Aka Danka wa Kwamitin sun haɗa da. Shirya takardar shawarwari bisa ga rahoton binciken da aka gabatar, neman karin bayani daga kwararru inda ya dace, da mikawa gwamnati rahoton karshe cikin makonni uku.
Kwamitin ya kunshi: Babban Lauyar Jihar kuma Kwamishiniyar Shari’a – Shugaban Kwamitin, Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya – Mamba, Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Lafiya ta Jihar Katsina – Mamba, Tsohon Babban Sakataren Tsaro da Harkokin Majalisar Zartaswa – Mamba, Safiyanu Maikano, tsohon Provost na Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Katsina – Mamba, Aminu Bello, Ofishin Gwamna – Sakataren Kwamitin
Kafa wannan kwamitin na cikin kokarin gwamnatin jihar Katsina na tabbatar da ingancin ilimin kiwon lafiya tare da bin ka'idojin da suka dace. Ana sa ran sakamakon binciken kwamitin zai taimaka wajen inganta horar da ma'aikatan kiwon lafiya a jihar.