Babangida Ya Nemi Gafara Kan Soke Zaɓen 1993

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20022025_135806_FB_IMG_1740059711236.jpg

Babangida Ya Nemi Gafara Kan Soke Zaɓen 1993

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya nemi gafarar ‘yan Najeriya kan soke zaɓen da Chief MKO Abiola ya lashe a ranar 12 ga Yuni, 1993.

Babangida ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa, taron da ya samu halartar tsoffin shugabannin ƙasa da kuma shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu.

A cikin jawabinsa, Babangida ya ce: “Na yi nadamar soke zaɓen 12 ga watan Yuni, 1993. A matsayina na shugaban ƙasa a lokacin, na ɗauki alhakin duk wani abu da ya faru a ƙarƙashin jagorancina.”

Bikin ƙaddamarwar ya samu jagorancin tsohon shugaban ƙasa, Janar Olusegun Obasanjo, yayin da Shugaba Tinubu ya kasance babban bako na musamman.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai tsoffin shugabannin ƙasa, Janar Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, da Goodluck Jonathan. Haka nan, tsoffin mataimakan shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo, da Yemi Osinbajo – wanda ya gabatar da sharhi kan littafin – sun halarta.

Sauran manyan shugabannin da suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, da tsohon shugaban Saliyo, Ernest Bai Koroma.

Follow Us