Gwamnatin Katsina Ta Kaddamar da Shirin ‘Runbun Sauki’ Don Rage Radadin Tashin Farashin Kaya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19022025_024543_FB_IMG_1739932815204.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Zaharaddeen Ishaq Abubakar, 18 ga Fabrairu, 2025 – 

Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da shirin Rumbun Sauki, wani shir da aka kirkiro domin saukaka wahalhalun tattalin arziki da al’ummar jihar ke fuskanta, musamman sakamakon tashin farashin abinci. An gudanar da taron kaddamarwar a zauren taro na Sakariyar Gwamnati, inda Gwamna Dikko Umar Radda ya jagoranci bikin tare da mataimakinsa, Faruq Lawal Jobe, Sakataren Gwamnati Abdullahi Garba Faskari, Shugaban Ma’aikata Alhaji Falalu Bawale, kwamishinoni, manyan jami’an gwamnati, da sauran masu ruwa da tsaki.

A jawabinsa, Gwamna Radda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar rage radadin wahalar tattalin arziki da ake fuskanta. Ya ce shirin Rumbun Sauki ba kawai rabon kayan abinci ba ne, wata cikakkiyar hanya ce ta tallafawa ma’aikata, masu ritaya, da gajiyayyu ta hanyar sayar da kayayyakin masarufi a farashi mai rahusa.

“Duniya na fuskantar matsalolin tattalin arziki, kuma hauhawar farashin kaya na haifar da matsin lamba ga iyalai da dama. Matsayinmu a matsayin gwamnati mai kishin jama’a shi ne mu dauki matakin rage radadin wahalar da ake fuskanta,” in ji gwamnan.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware sama da naira biliyan hudu (₦4bn) domin aiwatar da shirin, wanda za a fara a yankunan Katsina, Funtua, da Daura, kafin a fadada shi zuwa kananan hukumomi 34 na jihar.

Gwamna Radda ya bayyana cewa za a yi amfani da tsarin biyan kudi na zamani ta hanyar katunan ATM da aka kera musamman domin shirin. Wannan zai taimaka wajen hana cin hanci da rarraba kayayyakin ga wadanda suka cancanta kawai.  Sana kuma kudaden kayayyakin za a rika cirewa daga albashin ma’aikata don rage wahalar biyan kudin kaya.

A jawabin sa, shugaban Ma’aikata, Alhaji Falalu Bawale, ya jinjinawa shirin, yana mai bayyana shi a matsayin wata babbar nasara ga jin dadin ma’aikata. Ya kara da cewa gwamnatin Gwamna Radda ta riga ta aiwatar da tsare-tsare da suka hada da mafi karancin albashi na ₦70,000, biyan fansho da garatuti ga ‘yan fansho.

Ya bukaci ma’aikata da masu ritaya da su rungumi shirin, tare da yin amfani da shi yadda ya kamata domin amfanin gaba daya.

Ma’aikatan gwamnati na matakin jiha da kananan hukumomi, da kuma masu ritaya, za su iya yin rajista ta hanyar ziyartar shafin yanar gizo www.katsinarumbunsauki.com.ng inda za su shigar da lambar tantance ma’aikatansu don tabbatar da cancantarsu.

Gwamna Radda ya gargadi duk wani jami’i da zai nuna son kai ko cin hanci wajen aiwatar da shirin, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

“Idan muka hada kai gaba daya, ciki har da sarakuna da shugabannin addini, za mu tabbatar da cewa kowa ya ci moriyar wannan shiri kuma babu wani dan jihar da zai ci gaba da fama da matsalar karancin abinci,” in ji gwamnan.

Shirin Rubutun Sauki ya zama wata sabuwar hanya ta tallafawa al’ummar Katsina, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar na aiki tukuru wajen rage radadin wahalar rayuwa a wannan mawuyacin lokaci.

Follow Us