Kungiyar Ci Gaban Daliban Tsangaya Ta Gudanar da Taron Kara Haɗin Kan Alarammomi, Malaman Tsangaya, Tare da Yin Kira ga Gwamnati da Iyayen Yara

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06022025_221012_FB_IMG_1738879747697.jpg

Muhammad Ali Hafiziy, Katsina Times 

A ranar Alhamis, 6 ga Fabrairu, 2025, Kungiyar Ci Gaban Daliban Tsangaya ta Najeriya (Modern Tsangaya Students Development Association of Nigeria), reshen Jihar Katsina, ta shirya taron ƙara wa juna sani da haɗin kai tsakanin alarammomi da malaman makarantun tsangaya. Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Malam Masa'udu Rafindadi, shugaban reshen ƙungiyar na Katsina. Babban manufar taron ita ce yin kira ga iyayen yara da gwamnati domin samar da tallafi ga makarantun tsangaya, tare da inganta ci gaban karatun Alƙur'ani mai girma.

A yayin taron, malamai da dama sun yi tsokaci kan matsalolin da ke damun makarantun tsangaya, musamman wajen rashin kayan more rayuwa kamar rumfuna, rijiyoyin burtsatse, da banɗakuna. Sun nuna damuwa kan halin ko-in-kula da ake nunawa a waɗannan fannoni, wanda hakan ke shafar jin daɗin dalibai da lafiyarsu.

Haka kuma, malamai sun yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, bisa ga ƙoƙarin da yake yi wajen kula da addini. Sun nemi a ƙara mai da hankali kan tsabtace yanayin makarantun tsangaya domin kare lafiyar dalibai da kuma inganta yanayin karatu.

A nasa jawabin, Sakataren ƙungiyar, Malam Dahiru, ya yi kira ga iyayen da ke kawo 'ya'yansu makarantun tsangaya da su riƙa ziyartar su don ganin halin da suke ciki. Ya nuna damuwa kan yadda wasu iyaye ke kawo yara makarantun tsangaya ba tare da kula da halin da suke ciki ba, har ma wasu ba sa ziyartar 'ya'yansu har sai an ba da su.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa wa makarantun tsangaya wajen samar da kayan more rayuwa da inganta yanayin karatu, domin tabbatar da ci gaban ilimin Alƙur'ani mai girma a tsakanin al'umma.

Follow Us