Dan Jihar Katsina Ya Zama Sarkin Yarbawan Arewacin Najeriya

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times  

An tabbatar da nadin Alhaji Muntari Sani, Sarkin Yarbawan Funtua, a matsayin Sarkin Yarbawan Arewa, wata sarauta mai daraja da ke wakiltar al'ummar Yarbawa mazauna Arewacin Najeriya. An sanar da nadin ne a yayin wata ziyara da tawagarsa suka kai fadar gwamnatin jihar Katsina ranar Laraba, 29 ga Janairu, 2025, inda aka gabatar da takardar nadin ga Gwamnan jihar Katsina ta hannun Mataimakin Gwamna, Malam Faruq Lawal Jobe.  

Malam Faruq Lawal Jobe, wanda ya karɓi tawagar a madadin Gwamna, ya yaba da wannan ci gaba da aka samu, yana mai cewa, "Wannan ba wai nasara ce ga Alhaji Muntari Sani kadai ba, har ila yau, wata gagarumar nasara ce ga jihar Katsina da ma al'ummar Yarbawa mazauna Arewacin Najeriya gaba ɗaya."

An shirya gudanar da bikin nadin sarautar ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar 15 ga Fabrairu, 2025, inda ake sa ran wakilan gwamnatin jihar Katsina za su halarta don tabbatar da goyon bayansu ga wannan muhimmin matsayi.  

Tawagar da ta raka Alhaji Muntari Sani zuwa fadar gwamnatin Katsina ta kunshi manyan jagororin al'ummar Yarbawa, ciki har da Injiniya Muntari Alimi, Sarkin Yarbawan Kano, da Tajuddeen, shugaban ma'aikatan Sarkin Yarbawan Kano.  

Haka nan, daga jihar Katsina, wasu fitattun shugabanni sun kasance cikin tawagar, cikinsu har da Dr. Iro Musa Anda Funtua da kuma Alhaji Ndanusa Yunusa Yakubu, Sarkin Nupawan Katsina, wanda kuma shi ne Sakataren Ƙasa na Ƙungiyar Intertribal Association of Nigeria.  

Nadin Alhaji Muntari Sani a matsayin Sarkin Yarbawan Arewa wani mataki ne da ke ƙara haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al'ummomi daban-daban a Najeriya, yana kuma nuni da yadda jihar Katsina ke ci gaba da zama cibiyar haɗin kan kabilu a Arewacin ƙasar.

Follow Us