DUK NIJERIYA BA TARON DA YAKE TARA MILIYOYIN AL’UMMA KAMAR MAULUDIN MAJMA’U AHBAB SHEIH IBRAHIM NIASS.
- Sulaiman Umar
- 23 Jan, 2025
- 35
DAGA DR. BILKISU YUSUF ALI AL-QALAM UNIVERSITY, KATSINA
Mauludin bana wanda kungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyas shi ne mauludi karo na 39 wanda ya yi dai-dai da shekarun Sheikh Ibrahim Niass shekara 125 kuma za a gudanar da mauludin a Kano. Gagarumin mauludi ne da ake shirya shi duk shekara don tunawa da Sheikh Ibrahim Niass da gabatar da wasu ayyuka na musamman da tunasarwa ga mabiya Darikar Tijjaniyya. A wannan shekarar, za a gabatar da Mauludin ne ranar 25/01/2025 a jihar Kano da yardar Allah.
TARIHIN MAULUDIN SHEHU NA QASA
An fara gudanar da wannan mauludin a shekarar 1986 shekara 39 da suka wuce .
WADANDA SUKA ASSASA MAULUDUN SHEHU NA KASA
‘Yan’uwa almajiran Sheikh Ibrahim Niass ne suka assasa wannan mauludi qarqashin jagorancin marigayi Sidi Ahmad Kulaha wanda ya zama mataimakin shugaba da Sheikh Dahiru Abubakar Kurmi Shugaba, An fara da haxuwa a yi karatun alqur’ani duk lahadi anan ofishin Sidi Ahmad Kaulaha da ke Lagos duk lahadi. Yayin da ake yin wannan karatun sai wani xan’uwa ya zo ya gansu ya tambayi su “wannan me suke yi” suka ce “karatun Al-qur’ani suke yi hadiyya ga Sheikh Ibrahim Inyas”. Sai ya ce “Antu ma majma’u Ahbab”. Daga nan ne ma wannan suna na qungiyar Majma’u Ahbab ya fito. Daga nan aka samu mutane haziqai qarqashin jagorancin Alhaji Garba Hamza da Sheikh Xahiru Abubakar da Alhaji Talle da Alhaji Sani Rogo da Sheikh Aliyul Gali da Alhaji Aminu da saura da yawa suka qara qaimi da rungumar al’amarin . A nan aka yi shawara a fara zaman mauludi. An fara wannan mauludi a Lagos duk shekara, tun ana yi a gida har aka fara yi a waje. Bayan likkafa ta ci gaba sai aka fara gudanar da Mauludin Shehu a babban wuri har ta kai an fara gudanar da mauludin a wajen jihar Lagos. A shekarar 1991 an yi mauludin Shehu a jihar Kaduna sai 1992 a Ibadan. A 1993 an yi a jihar Kano. 1994 an kai mauludin Ilorin, 1995 aka yi a Sakkwato. A shekarar 1996 aka je Osun 1997 aka je Filato haka dai aka yi ta tafiya ana zagayawa har shekaru huxu baya aka yi a jihar Bauchi da jihar jigawa da da Jihar Sakkwato. Shekarar 2022 an yi a jihar Zamfara a shekarar 2023 aka yi a jihar Kebbi sai kuma 2024 a birnin Tarayya Abuja. A yayin maulud na bara a Abuja shugaban Majma’u na Qasa Sheikh Tijjani Sani Auwalu ya isar da saqon gwamnatin jihar Kano kan tana son a shekara mai zuwa a gudanar da Mauludin Shehu a Kano kuma qarqashin Sarkin Kano kuma Halifan Tijjaniyya Alh Dr Muhammadu Sunusi na biyu. Kuma daga baya aka sanar da amincewar yin mauludin a Kano.
YADDA MAULUDIN MAJMA’U YAKE JIYA DA YAU
Qungiya ta yi matuqar albarka an samu cigaba a al’amuranta, duba da tun da aka fara yin Mauludin Shehu duk shekara ba a daina ba, ba a yi fashi ba, kullum cigaba a ke samu qara havaka mauludin yake yi, qara tagomashi yake yi , mutane qara himma a hakar suke yi, babu wani taro kowanne iri ne a qasar nan da yake tara jama’a kamar mauludin Shehu wannan ba qaramar nasara ce ba masu gudanar da taron mauludin da masu halarta. Wani abun burgewa Tunda ake yin mauludin Shehu qarqashin shugabancin qungiyar Majma’u babu wani abu na vatanci ko assha ko rashin jin daxi da ya tava biyo bayan mauludin sai ma na san barka.Wannan ba karamar albarka ce ba. “Taron da aka fara a xaki da karatun alqur’ani yau ana yinsa a jihohi wannan albarkace ta Shehu Ibrahim Kuma albarka ce ta almajiran Shehu Ibrahim. Wannan qungiya ta yi matuqar albarka Sheikh Abdullahi Inyas ya sa mata hannu ya sa mata tambari kuma ya sa hannu ya ba da izini akan mazaje jajirtattu irin su Sheikh Xahiru Abubakar da suka tsayawa qungiyar , wanda yake shugabantarta tun a wannan shekarun har zuwa shekarar 2022 da Allah ya yi masa rasuwa.Allah ya saka masa da Alheri shi da Sidi Kaulaha” Inji shugaban Majma’u na qasa Sheikh Tijjani Sani Auwalu kuma kwamishina na Addinai na jihar Kano.
MAULUDIN SHEHU NA QUNGIYAR MAJMA’U YANA DA BAMBANCI DA DUKKANIN MAULUDIN SHEHU DA AKE GUDANARWA A QASAR NAN
Wannan mauludi na musamman ne , wanda ya haxa kowanne vangare, kowanne xan zawiyya kowanne gidan Shehi duk an haxu a inuwa guda. Kowanne Shehi yana zuwa wannan mauludi kuma in an zo mauludin kowa yana jin wannan maulidn nashi ne babu wariya. Wannan mauludi ya haxe kowanne xan Tijjaniya kuma xan Faira Shehu Ibrahim wuri xaya don haka ana mauludin ne da yawu xaya. Duk Almajiran Shehu na haqiqa suna tare da wannan mauludin kuma suna zuwa da su da muridansu gabaki xaya,
DALILAN DA SUKA JANYO WANNAN NASARA
Dalilai da dama su suka haifar da wannan nasara da ake samu duk shekara yayin wanan maulud da majma’u take shiryawa amma daga ciki akwai:
“Qarfin almajiran Shehi Ibrahim Inyas suke da shi da yawan da suke da shi da iya tara jama’a da tafiyar da su cikin amana da adalci da haxin kansu da soyayyarsu da iya mu’amalarsu shi ne silar wannan nasarar. Haka Goyon bayan da manyan Shehunnanmu suke bayarwa shi ma nasara ne. Don kuwa duka taron almajiran waxannan shehunnan ne da masoya ke zuwa . Haxin kai shi ma yana cikin qashin bayan nasarar wannna taron da ake yin a mauludi” Cewar tsoyon kwamishinan addinai na jihar Kano kuma malami a jami’ar Bayero ta Kano, Imam Dr Muhammad Nazifi Bichi. Taro ne da ke kawo cigaban al’umma, ba ma iya ‘yan xariqar Tijjaniya ba ga dukkan musulmi. Taro ne da yake kawo cigaba a tattalin arziqin qasa inda a wannan kwanakin da za a yin a taron al’umma daga ko’ina ciki da wajen qasar nan kan yi tururuwa don su halarta. Babu wani taro a cikin qasar Nijeriya da wajenta da yake tara ‘ya’yan Shehu bayan maulud xin Kaulaha, sai mauludin da Majma’u da take gabatarwa. “Tun zamanin Shehu Abdullahi tun ana zuwa mutum goma, ishirin, akwai shekarar da ta zo sai da muka zo da mutum tamanin da wani abun daga Kaulaha. Kuma duk shekara ne ‘ya’yan Shehu Ibrahim da jikoki da muqaddamai da almajiran Shehu suna tasowa daga Sinigal su zo. Gwamnati tana samun damar xaukar wannan taro a mafi yawan lokuta saboda kwadayin samun wannan albarka da Shehu Ibrahim don haka suke ba da gudummawa” Inji Sheikh Tijjani Sani Auwalu.
FATANMU
Babban fatanmu a yi taro lafya a kammala lafiya a samu falalar da ake samu ta zumumci da tausayi da taimakon juna da qara jin wasu halaye na Sheikh Ibrahim Inyas da kuma fatan a yi aiki da duk abin da aka ji. Waxanda suka rasu a wannan qungiyar da sauran almajiran Shehu,amin.