AJIYE AIKI: Ofishin Sakataran Gwamnatin Jihar Katsina Ya Karrama Babban Sakatare, Alhaji Salisu Abdu
- Katsina City News
- 03 Jan, 2025
- 96
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Juma’a, 3 ga Janairu, 2024, ofishin Sakataran Gwamnatin Jihar Katsina ya gudanar da taron bankwana da karrama Alhaji Salisu Abdu, Babban Sakatare mai kula da harkokin Majalisa da Tsaro, wanda ya kammala aikinsa a gwamnatin jihar. Taron ya gudana a dakin taro na ofishin Sakataran Gwamnati, Abdullahi Garba Faskari, wanda ke cikin sakatariyar gwamnatin jihar Katsina.
Da yake gabatar da jawabinL, Sakataran Gwamnati, Abdullahi Garba Faskari, ya yaba da jajircewar Alhaji Salisu Abdu a yayin gudanar da ayyukansa na gwamnati. Ya bayyana cewa Alhaji Salisu ya zama abin koyi wajen gaskiya, rikon amana, da sadaukarwa a harkokin gwamnati. Faskari ya kuma yi masa fatan alheri tare da addu’ar Allah ya ci gaba da taimaka masa a rayuwa bayan ritaya.
A nasa bangaren, Alhaji Salisu Abdu ya nuna matukar farin ciki bisa karramawar da aka shirya masa. Ya yi godiya ga ofishin Sakataran Gwamnati da dukkan ma’aikatan da suka kasance tare da shi a tsawon lokacin da ya yi yana aiki. Ya bayyana cewa hadin kan da ya samu daga ma’aikatan ofishin ne ya ba shi damar cimma nasarori da dama. A karshe, ya yi addu’ar Allah ya ba dukkan ma’aikatan ikon kammala aikinsu lafiya.
Taron ya samu halartar manyan jami’ai da ma’aikata daga bangarori daban-daban na gwamnatin jihar, wadanda suka gabatar da jawabai na yabo da fatan alheri ga Alhaji Salisu Abdu. Da dama sun bayyana shi a matsayin mutum mai hakuri, dattako, da jajircewa wajen aiki, suna mai tabbatar da cewa ya bar babbar kyakkyawar alama a ofishin.
Taron ya kasance cike da nishadi da karramawa, inda aka mika masa kyaututtuka na musamman a matsayin girmamawa bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Katsina.
Alhaji Salisu Abdu ya yi ritaya daga aikin gwamnati tare da samun karramawa daga ofishin Sakataran Gwamnatin Jihar Katsina, abin da ya nuna girmamawar da gwamnatin jihar ke da shi ga sadaukarwar ma’aikatanta.