Shugaban Ƙungiyar Dikko Project Ya Kai Ziyarar Bangirma Ga Dan Majalisar Katsina
- Katsina City News
- 30 Dec, 2024
- 168
A ranar Asabar, 28 ga Disamba, 2024, Shugaban Ƙungiyar Dikko Project kuma shugaban kamfanonin Gafai Communication da Gafai Restaurant, Hon. Musa Gafai, ya kai ziyarar bangirma ga Dan Majalisar Jihar Katsina mai wakiltar Karamar Hukumar Katsina, Hon. Abubakar Aliyu Albaba. Ziyarar ta gudana ne a gidan Hon. Albaba da ke Unguwar Albaba cikin birnin Katsina.
Hon. Musa Gafai ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce tabbatar da zumunci da tattaunawa kan yadda za a kara kawo ci gaba mai ma’ana ga al’umma.
A nasa bangaren, Hon. Abubakar Aliyu Albaba ya nuna farin ciki da godiya bisa wannan ziyara, tare da jaddada alkawarin yin aiki tare da Hon. Gafai domin amfanar jama’a, bisa yardar Allah.